An kashe yan ta’addan Boko Haram 3 a Borno – Rundunar soji

An kashe yan ta’addan Boko Haram 3 a Borno – Rundunar soji

Dakarun sojin Operation Lafiya Dole dake yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar a ranar Talata, 28 ga watan Agusta sun kashe yan ta’addan Boko Haram uku a wani harin bazata da yan ta’addan suka kai a hanyar Gulumba Gana-Masa – Dikwa dake karamar hukumar Dikwa na jihar Borno.

Rundunar sojin Najeriya na Operation Lafiya Dole sun kashe yan ta’addan Boko Haram a wani harin bazata a jihar Borno.

Jin kadan kafin harin bazatan, rundunar wadanda ke zarya sun gano wasu bama-bamai da ya ta’addan suka binne a kasa a hanyar.

An kashe yan ta’addan Boko Haram 3 a Borno – Rundunar soji

An kashe yan ta’addan Boko Haram 3 a Borno – Rundunar soji
Source: Facebook

Yayinda dakarun ke kokarin kwance bama-baman sai yan ta’addan suka kawo harin bazata amma sojojin sun yi nasara akansu inda suka kashe yan ta’adda uku yayinda sauran suka tsere da harbin bindiga.

KU KARANTA KUMA: Zan kashe kaina idan Buhari ya fadi a zaben 2019 – Wani mutumin Abuja yayi barazana

An kashe yan ta’addan Boko Haram 3 a Borno – Rundunar soji

An kashe yan ta’addan Boko Haram 3 a Borno – Rundunar soji
Source: Facebook

Rundunar sun kwato bindigogi AK 47 guda biyu, bindigar mashin guida da kuma mujalla daga yan ta’addan.

Jami’in soja daya ya samu rauni inda yake samun kulawar likitoci a yanzu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel