An kone wani Fasto, matar sa da yara 3 a sabon rikicin Barkin Ladi

An kone wani Fasto, matar sa da yara 3 a sabon rikicin Barkin Ladi

An kone Rabaran Adamu Gyan Wurim, babban Fasto a Cocin garin Foron dake karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato.

Ana zargin wasu makiyaya ne suka kone Fasto Wurim tare da matar sa da 'ya'yan su uku. Kazalika an kone Cocin da Fasto Wurim ke jagoranta.

Rahotanni sun bayyana cewar 'yan bindigar da suka kashe Faston da iyalinsa, sun kashe wasu Makwabtan gidan Faston biyu kafin zu zarce kauyen Dorawa, inda suka kara kaddamar da wasu hare-haren.

An kone wani Fasto, matar sa da yara 3 a sabon rikicin Barkin Ladi

An kone wani Fasto, matar sa da yara 3 a sabon rikicin Barkin Ladi
Source: Depositphotos

Faston da iyalinsa sun mutu ne bayan 'yan bindigar sun kewaye gidansu tare da cinna masa wuta.

DUBA WANNAN: Magoya bayan Kwankwaso sunyi hatsari a hanyarsu ta zuwa Abuja

Kazalika, an garzaya da wata zuwa asibiti bayan alburushi ya ji mata ciwo.

Dan majalisar dokokin jihar Filato dake wakiktar mazabar Barkin Ladi, Honarabul Peter Gyendeng, ne ya tabbatar da kai harin ga manema labarai tare da bayyana cewar yana kan hanyar sa ta zuwa mazabar tasa domin jajantawa jama'a iftila'in da ya afka masu.

Sai dai hukumar 'yan sanda da da hadakar jami'an tsaro ta Ofireshon save Haven (STF) basu tabbatar da afkuwar kai harin ba a daidai lokacin da aka kammala hada wannan rahoto.

Hare-haren na zuwa ne cikin kasa da sa'o'i 24 bayan tsohon gwamnan jihar Filato, Sanata Jonah Jang, ya kaddamar da takarar sa ta shugaban kasa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel