Tsohon Gwamna Lamido yayi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari

Tsohon Gwamna Lamido yayi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa watau Alhaji Sule Lamido ya soki Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Lamido yana cikin masu neman takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP.

Tsohon Gwamna Lamido yayi kaca-kaca da Gwamnatin Buhari

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido
Source: UGC

Sule Lamido ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai iya duakar adawar ‘Yan siyasar kasar nan. Tsohon Gwamnan yace Shugaban kasa Buhari bai iya hakuri da ‘Yan adawa saboda tarbiyyar sa na gidan Soja.

‘Dan takarar Shugaban kasar yayi wannan bayani ne a Jihar Bauchi lokacin da ya ziyarci manyan Jam’iyyar PDP. Lamido ya kuma nemi mutanen Jihar Bauchi su marawa wanda PDP ta tsaida takara baya a zabe na 2019.

KU KARANTA: Wani ya nemi Magoya bayan Buhari su zayyano aikin da aka yi a harkar kiwon lafiya

Lamido yace a lokacin da Atiku da Kwankwaso da su Saraki su ka bar PDP, sai aka rika yi masu kallon Ma’asumai a APC, yanzu kuma dai an koma kiran su barayi bayan sun sake sauya-sheka yayin da ake yabon irin su Akpabio.

Tsohon Gwamnan yake cewa Gwamnatin Buhari ta kyale ‘Yan APC su na cin karen su babu babbaka yayin da aka hada wadanda su ka bar Jam’iyyar APC da Hukumar EFCC mai yaki da masu yi tattalin arzikin kasa zagon-kasa.

Dazu ne ku ka ji cewa ana zargin cewa Shugaban Kasa Buhari yana kokarin takurawa ‘Yan adawa. An yi can ne a kan Buhari na hana tsohon Gwamna Kwankwaso kaddamar da shirin tsayawa takara a Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel