Fadar Shugaban 'Kasa ta barrantar da kanta daga kalaman Hadimin shugaba Buhari

Fadar Shugaban 'Kasa ta barrantar da kanta daga kalaman Hadimin shugaba Buhari

A ranar Talatar da ta gabata ne fadar shugaban kasa ta barrantar da kanta tare da yin hannun riga da kalaman shugaban kwamitin bayar da shawara ga shugaban kasa akan harkokin rashawa, Itse Sagay, dangane da takaddamar takardun bogi na Ministar Kudi, Kemi Adeosun.

Rahotanni daga kafofin watsa labarai da dama na kasar nan sun ruwaito cewa, ana zargin Ministar ta shugaban kasa Muhammadu Buhari da rashawa ta amfani da takardun bogi dake nuna shaidar hukumar bautar kasa ta NYSC, bayan bankaɗa gami da fallasa da jaridar Premium Times ta aiwatar a watan Yulin da ya gabata.

A yayin da ake ci gaba da huro wuta kan tsige Ministar, shugaban kwamitin a ranar 9 ga watan Agusta da ta gabata ya yi kira kan rashin goyon bayan tsige hadimar ta shugaba Buhari sakamakon muhimmancinta a wannan gwamnatin gami da kwarewa bisa aiki.

Fadar Shugaban 'Kasa ta barrantar da kanta daga kalaman Hadimin shugaba Buhari

Fadar Shugaban 'Kasa ta barrantar da kanta daga kalaman Hadimin shugaba Buhari
Source: Twitter

Da yake ci gaba da jaddada matsayar sa ta kare Ministar ta shugaban kasa, Farfesa Sagay ya kuma jaddada cewa rashin gudanar da bautar kasa ta Ministar ba ya da wani muhimmanci kamar yadda aka dabbaka a kasar nan.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, wannan laifi da ake zargin Ministar ya sabawa sashe na 13 cikin dokoki na hukumar bautar kasa ta Najeriya, inda bayan kwanaki fiye da 50 na wannan fallasa ba bu wanda ya ce uffan tsakanin shugaban kasa da kuma Ministar sa.

KARANTA KUMA: Za mu tabbatar da girmama Doka da 'Ka'idoji yayin Zaɓen fidda gwani - Oshiomhole

A yayin martani dangane da wanna tabokara, kakakin shugaban kasa Mista Femi Adesina ya bayyana cewa, kalaman Farfesa Sagay ba su da alaka ta kusa ko ta nesa da shugaban kasa Buhari, inda ya ce gwamnatin su na ci gaba da gudanar da bincike akan lamarin.

Mista Adesina ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai na kafar watsa labarai ta Channels TV a ranar Talatar da ta gabata, inda ya ke cewa Farfesa Sagay yayi wannan furuci bisa ra'ayi na karan kansa kuma ba ya dangantuwa zuwa ga shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel