Da ace Trump mutumin Najeriya ne, da Buhari ya kama sa - Fayose

Da ace Trump mutumin Najeriya ne, da Buhari ya kama sa - Fayose

Mun samu labari cewa Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Peter Fayose ya kuma sukar Shugaban kasa Buhari bayan Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya caccaki Shugaban na Najeriya.

Da ace Trump mutumin Najeriya ne, da Buhari ya kama sa - Fayose

Fayose ya sa baki bayan Trump ya caccaki Shugaba Buhari
Source: Depositphotos

Gwamna Ayodele Fayose na Ekiti wanda ya saba sukar Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa da ace Donald Trump mutumin Najeriya ne, da tuni Shugaban kasar na Najeriya ya maka shi kara a gaban Kotu.

Hakan na zuwa ne bayan an ji labarin cewa Shugaban na Amurka yayi kaca-kaca da Shugaba Buhari bayan wata ganswa da su kayi kwanaki. Ana kishin-kishin din Shugbaba Trump yace bai son kara haduwa da mutum irin Buhari a Duniya.

KU KARANTA: Najeriya ce hedikwatar talaucin Duniya - Shugabar Ingila

Gwamnan ta shafin sa na Tuwita ya nuna cewa Shugaba Buhari mutum ne maras hakuri da kuma nunawa sauran ‘Yan siyasar bakar adawa. A cewar Gwamnan, da Buhari zai iya, da ya nemi ayi masa maganin Shugaban kasa Trump.

Ana dai zargin Gwamnatin Buhari da hana ‘Yan adawa sakat a Najeriya wanda kwanan nan ne aka hana Kwankwaso farfajiyar Eagles Square a cikin Garin Abuja inda ya shirya kaddamar da shirin tsayawa takarar kujerar Shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel