Za mu tabbatar da girmama Doka da 'Ka'idoji yayin Zaɓen fidda gwani - Oshiomhole

Za mu tabbatar da girmama Doka da 'Ka'idoji yayin Zaɓen fidda gwani - Oshiomhole

Jam'iyyar APC ta sha alwashi na tabbatar da kiyaye duk wata 'ka'ida gami da girmama duk wata doka ta tsarin zaɓe, gaskiya da kuma adalci tare da tabbatar da kwararar romon dimokuradiyya yayin gudanar da zaɓenta na fidda gwani a watan gobe.

Shugaban jam'iyyar na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, shine ya bayar da wannan tabbaci yayin ganawar sa a manema labarai na fadar shugaban bayan zaman jiga-jigan jam'iyyar da aka gudanar a daren ranar Talatar da ta gabata.

Oshiomhole ya bayar da tabbacin cewa ganawar su ta tattauna kan al'amurran da suka shafi zaɓen fidda gwani na jam'iyyar da kuma jadawali na tsare-tsaren gudanar babban zabe na 2019 kamar yadda hukumar ta zabe ta kasa INEC ta fitar a watan Janairun da ya gabata.

Jadawalin gudanar da zaben kamar yadda hukumar INEC ta fitar da sanadin shugabanta, Farfesa Yakubu Mahmoud, ya bayyana cewa dukkanin jam'iyyun kasar nan za su gudanar da zaben fidda gwani na kujerar shugaban kasa, gwamnoni da kuma 'yan majalisun dokoki da na tarayya daga ranar 18 ga watan Agusta zuwa ranar 7 ga watan Oktoba na 2018.

Za mu tabbatar da girmama Doka da 'Ka'idoji yayin Zaɓen fidda gwani - Oshiomhole

Za mu tabbatar da girmama Doka da 'Ka'idoji yayin Zaɓen fidda gwani - Oshiomhole
Source: Depositphotos

A cewar Oshiomhole, jam'iyyar ta APC za ta tabbatar da kiyaye dukkanin wata doka gami da ka'idojin hukumar zabe sakamakon tanadi na kundin tsarin gudanar da zabe na kasa.

Kazalika jam'iyyar ta sha alwashin tabbatar da gaskiya da kuma adalci yayin zaben fidda gwani a taron da ta gudanar wanda mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da kuma jiga-jigan jam'iyyar suka halarta.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya tana neman taimakon Bankin Duniya da Bill Gates kan Hukumar NHIS

Sauran wadanda suka halarci taron sun hadar da gwamnonin jihar Borno, Jigawa, Neja, Filato, Adamawa, Ondo, Kano, Ogun, Oyo, Katsina, Osun, Yobe, Nasarawa, Kebbi, Imo da kuma Legas.

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Mista Segun Oni, shugaba na majalisar wakilai mai rinjaye Femi Gbajabiamila; tsohon gwamnan jihar Ebonyi Mista Martin Elechi; tsohon gwamnan jihar Borno Ali Sheriff; Buba Marwa, Janar Lawrence Onoja, Cif Jim Nwobodo da kuma Sanata Kabiru Gaya na jihar Kano sun halarci taron da aka gudanar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel