Yanzu Yanzu: Saraki ya gana da Goodluck Jonathan a Abuja

Yanzu Yanzu: Saraki ya gana da Goodluck Jonathan a Abuja

- Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan yace yana ganawa da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki

- An tattaro cewa manyan shugabannin sun gana ne a babban birnin tarayya, Abuja

- Zuwa yanzu babu wani cikakken bayanin kan ganawar tasu

Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, wanda ya bayyana kudirinsa na takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019, na ganawa da tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Haramci akan kodin da tramadol ya sanya ayyuka mutane 25,000 cikin hatsari – Kungiya

Yanzu Yanzu: Saraki ya gana da Goodluck Jonathan a Abuja

Yanzu Yanzu: Saraki ya gana da Goodluck Jonathan a Abuja
Source: Depositphotos

Zuwa yanzu dai babu cikakken bayani akan dalilin ganawar nasu.

A halin yanzu, Legit.ng ta rahoto cewa Saraki yace yana nazari akan karawa da Shugaban kassa Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Legit.ng ta tattaro cewa Saraki a wani hira da akayi da shi a gidansa na Abuja, yace: “Ina nazari akan hakan. Nayi imanin cewa zan iya kawo chanji.

“Jam’iyyar PDP ta koyi darasinta daga faduwar da tayi a 2015, kuma ina ganin jam’iyyar APC bata koyi darasi daga nasararta ba.

“Muna da dama tare da irin dan rakarar shugaban kasa da zai iya gabatar da irin shugabancin da ake so. Jam’iyyar na da dama mafi inganci waje shugabantar kasar zuwa hanya madaidaiciya."

A halin da ake ciki, mun ji cewa yyuka sun kachame a babban sakatariyar jam’iyyar Democratic Party (PDP) dake Abuja a jiya, Talata, 28 ga watan Agusta yayinda jam’iyyar ta fara siyar da fam din ra’ayi tsayawa tkara ga yan siyasar dake son takara a zaben 2019 a inuwarta.

Yayin da yan takara da dama suka biya kudin fam a asusun banki, wasu sun biya ne ta na’urar POS.

Daga cikin wadanda suka yanki fam din a jiya sun hada da Gwamnan jihar ombe,Ibrahim Dankwambo, wanda ke neman takarar kujerar shugabancin kasa a karkshn PDP a zaben 2019.

Bayan Dankwambo, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ma ya yaki fam din taarar shugabancin kasa a jam’iyyara jiya. Dukkansu su biyun sun biya naira miliyan biyu na nuna ra’ayi da kuma naira mliyan 10 na fam din.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel