Zaben 2019: Dankwamboda Lamido sun yanki fam din takarar shugabancin kasa a PDP

Zaben 2019: Dankwamboda Lamido sun yanki fam din takarar shugabancin kasa a PDP

Ayyuka su kachame a babban sakatariyar jam’iyyar Democratic Party (PDP) dake Abuja a jiya, Talata, 28 ga watan Agusta yayinda jam’iyyar ta fara siyar da fam din ra’ayi tsayawa tkara ga yan siyasar dake son takara a zaben 2019 a inuwarta.

Rahotanni sun nuna cewa babban jam'iyyar adawar kasar, PDP ta fara siyar da fam din takara a karkashinta.

Yayin da yan takara da dama suka biya kudin fam a asusun banki, wasu sun biya ne ta na’urar POS.

Daga cikin wadanda suka yanki fam din a jiya sun hada da Gwamnan jihar ombe,Ibrahim Dankwambo, wanda ke neman takarar kujerar shugabancin kasa a karkshn PDP a zaben 2019.

Bayan Dankwambo, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ma ya yaki fam din taarar shugabancin kasa a jam’iyyara jiya. Dukkansu su biyun sun biya naira miliyan biyu na nuna ra’ayi da kuma naira mliyan 10 na fam din.

Zaben 2019: Dankwamboda Lamido sun yanki fam din takarar shugabancin kasa a PDP

Zaben 2019: Dankwamboda Lamido sun yanki fam din takarar shugabancin kasa a PDP
Source: Depositphotos

Lamido ya mallaki fam dinsa ne ta hanu wakilinsa a sakatariyar jam’iyyar na asa, Wadata House.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya lashe zaben 2019 ya gama – Dan majalisa Buhari ya lashe zaben 2019 ya gama – Dan majalisa

Koda dai an tattaro cewa tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa ya mallaki fam din takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar a jiya, babu tabbaci akan hakan a daidai lokacin wannan rahoto.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa jam’iyyar PDP za ta sawakewa ‘Yan mata da kuma Matasa da ke shirin takara a karkashin Jam’iyyar adawar a zaben 2019.Hakan zai sa a samu karuwar matasa da mata a mulki.

Kwanan nan ne babban Jam’iyyar adawar ta fitar da farashin fam din takara a zabe mai zuwa na 2019. Majalisar zartarwa na PDP ta yanke hukuncin rage farashin fam din takarar ‘Yan Majalisa domin ba matasa damar shiga takara.

Yanzu dai PDP ta rage kudin fam din tsayawa takarar kujerar Majalisar Tarayya daga Naira Miliyan 2 zuwa Naira Miliyan 1. Jam’iyyar ta dauki wannan mataki ne bayan an rage shekarun tsayawa takarar kujerar Majalisar Tarayya a kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel