Ku guji makircin watan Maris: Limamin Katolika ya gargadi yan Nigeria

Ku guji makircin watan Maris: Limamin Katolika ya gargadi yan Nigeria

-Babban limamin katolika a jihar Legas ya yi gargadin cewa akwai wasu batagari dake shirin kwantar da kasar kafin 2019

- Anthony Cardinal ya buga misalin abubuwan da ke faruwa a kasar da labarin Julius Caesar na littafin da Shakespeare ya rubuta

- Daga karshe limamin katolikan ya bukaci yan Nigeria da su zabi cancanta ba tare da duba addiji, yare ko jam'iya ba

Wani babban limamin katolika na jihar Legas (Mai ritaya), Anthony Cardinal Olubunmi Okogie, ya yi gargadin cewa akwai wasu bata garin yan siyasa da ke kokarin ganin sun tarwatsa kasar kafin nan da zaben 2019, yana mai kira ga al'uma da su guji yin zabe don addini, yare ko jam'iya.

Cardinal Okogie, cikin wata wasika mai taken: "Ayi hattara da makircin watan Maris", ya ce: "Babu wani masoyin Nigeria na hakika da zai yarda ya zama silas zubar da jini".

Babban limamin katolikan ya ce: "Zai zama babban makarci a garesu a matan Maris, lokacin da masu yin magana da yawun shugaban kasa da gwamnoni ba zasu iya cewa uffan ba. Yanzu da muke tunkarar wata shekarar ta zabe, za'a fara samun bulluwar sabbin makirce makirce, kamar dai yadda yake a labarin Julius Caesar, na Shakespeare.

"Idan muka kwatanta labarin da abinda ke faruwa yanzu, zamu ga cewa Julius Caesar ne zai zama a madadin Nigeria; yan siyasar Roma kuwa da suka shirya tuggun kashe shi, su ne zasu wakilci mafi rinjayen jama'ar Nigeria, in da Brutus, dan siyasar da ya fake da shi abokin Caesar ne, zai zama wakilin yan siyasar dake nuna suna son Nigeria a fili, amma a zuciya ba haka bane.

Ku guji makircin watan Maris: Limamin Katolika ya gargadi yan Nigeria

Ku guji makircin watan Maris: Limamin Katolika ya gargadi yan Nigeria
Source: Facebook

KARANTA WANNAN: 2019: Kwankwaso ya kwace birnin tarayya yayinda yake kaddamar da yakin zabe a yau

"Nigeria, kamar dai Caesar, ya zamar mata wajibi ta yi hattara da makircin watan Maris. Mun dai ga yadda rikicin Boko Haram ya kasance. Mun kuma dai ga yadda ake yiwa wasu jama'a a sassa daban daban yankan rago, saboda rikicin manoma da makiyaya.

"A faruwar irin hakan, mai makon daukar mataki, sai kowa yayi biris kamar dai babu abinda ya faru. Muna jin yadda ake shigowa da makamai a kasar, misalin lamarin da ya faru a kwana kwanan nan, amma anyi shiru da maganar. Abin tambayar a nan shine; Shin me za'ayi da wadannan makamai da aka kama lokacin da za'a shigo da su?

"Me yasa har yanzu wadanda suka kutsa majalisar dokoki ba'a gano su ba? Me ya sa gwamnati ta ke yin biris akan irin wadannan muhimman batutuwa?

"La'akari da abubuwan dake faruwa yanzu, akwai take taken wasu bata gari dake son tarwatsa kasar nan kafin zaben 2019. Ya zama wajibi mu zamo masu sa ido akan yan siyasarmu dama masu rike da mukaman gwamnati."

Babban limamin katolikan ya bayyana cewa, wannan ne lokacin da yakamata 'yan Nigeria su zabi cancanta, ba wai wadanda zasu lalata kasar kuma su gudu su barta ba. A cewarsa, suna zaune suna kallon abubuwan da ke faruwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel