Najeriya ce shelkwatar talauci ta duniya – Firaminstar kasar Ingila

Najeriya ce shelkwatar talauci ta duniya – Firaminstar kasar Ingila

A jiya, Talata, ne Theresa May, firaministar kasar Ingila ta ce Najeriya ce yanzu haka a sahun gaba a yawan talakawa a duniya.

Da take Magana jiya, Talata, a birnin Cape Town na kasar Afrika ta Kudu, Theresa May ta bayyana cewar nahiyar Afrika ce a gaba wajen yawan mutanen da rigingimu suka raba da muhallinsu.

Har ila yau ta kara da cewa nahiyar Afrika ce a gaba wajen yawan talakawa a duniya, tare da bayyana cewar a kall mutane kimanin miliyan 87 ne ke fama da matsanancin talauci a Najeriya.

Najeriya ce shelkwatar talauci ta duniya – Firaminstar kasar Ingila

Buhari da Theresa May
Source: Depositphotos

Tattalin arzikin Najeriya na farfadowa, amma duk da haka akwai mutane miliyan 87 na rayuwa a kasa da dalar Amurka $1 a kowacce rana, hakan ya saka kasar a gaba wajen yawan talakawa a duniya,” a cewar Firaministar ta kasar Ingila.

Ko a watan Yuni said a wata cibiyar Turai, Brookings Institution, ta bayyana cewar Najeriya ta doke kasar Indiya a yawan talakawa a duniya.

DUBA WANNAN: Majalisar dinkin duniya ta zakulo matsalar dake rura wutar rikicin Boko Haram

A wancan lokacin, gwamnatin Najeriya ta bukaci ‘yan Najeriya da suyi watsi da rahoton saboda an tattara alkaluman da aka yi amfani da su ne lokacin da kasar ke cikin halin matsin tattalin arziki.

Theresa May ta bayyana cewar akwai bukatar samar da aiki ga mutane 50,000 kullum a Afrika har zuwa shekarar 2035 domin shawo kan matsalar talauci a nahiyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel