Dalilan da suka sanya na koma APC - Uduaghan

Dalilan da suka sanya na koma APC - Uduaghan

- Kafin gudanar da zaben 2019, kasuwar sauya sheka na cigaba da ci

- Wani jigo a PDP ya sanar da ficewarsa

- Sai dai ya bayyana cewa yayi hakan don cigaban yankin

Tsohon gwamnan jihar Delta kuma jigo a cikin jam’iyyar PDP Emmanuel Uduaghan, ya wanke kafarsa tsam ya tsoma ta cikin jam’iyyar APC. A cewarsa ya jefar da kwallon mangwaro ne domin ya huta da kuda.

Dalilan da suka sanya na koma APC - Uduaghan

Dalilan da suka sanya na koma APC - Uduaghan
Source: Facebook

Shi dai Uduaghan ya taba zama gwamnan jihar Delta dake da tarin arzikin man fetir, daga shekarar 2007 zuwa 2015, kuma ya daya daga cikin mahalarta taro shugabannin jam’iyyar APC na kasa da ya gudana a fadar shugaban kasa, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Siyasa magana ce ta ra'ayi, kuma na fito daga yankin Niger-Delta, wanda kuma ina daga cikin wadanda ke kokarin magance wutar rikicin dake tasowa a yankin".

KU KARANTA: Magoya bayan Kwankwaso sunyi hatsari a hanyarsu ta zuwa Abuja

Shugaban kasa yana bukatar manyan mutanen da suka fito daga yankin Niger Delta, domin mun jima muna tattaunawa akan yadda za'a habbaka cigaban kasar nan.

Da ya juya batun cigaban da shugaban kasa ya kawo yankinsa, ya ce a karon farko kenan da aka samu hanyar layin dogo ta shigo har cikin jihar Delta. Baya ga haka kuma ga ciyarwar da ake wa daliban makarantun firamare a fadin jihar tasu.

Idan za'a iya tunawa dai a kwanakin baya ne aka dinga rade-radin ficewar Emmanuel Uduaghan daga PDP zuwa APC, amma taron da masu ruwa da tsaki a matakin kasa na jam’iyyar APC suka yi a daren jiya Talata ne ya raba wannan gardamar.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel