Rashin adalci da nuna son kai na jam'iyyar APC ya sanya na sauya sheka zuwa PDP - Ayorinde

Rashin adalci da nuna son kai na jam'iyyar APC ya sanya na sauya sheka zuwa PDP - Ayorinde

A ranar Talatar da ta gabata ne wani dan majalisa mai wakilcin mazabar Owo/Ose ta jihar Ondo, Mista Bode Ayorinde, ya bayyana cewa rashin adalci gami nuna wariya da kuma son kai na jam'iyyar APC ya tursasa shi barin jam'iyyar zuwa PDP.

Mista Ayorinde yana daya daga cikin tsaffin mambobin jam'iyyar APC na majalisar dokoki ta tarayya da suka sauya sheka a kwanan-kwanan nan zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Dan majalisar ya bayyana hakan ne a shelkwatar jam'iyyar ta PDP dake babban birni na Akure a jihar Ondo, a yayin da yaje sayen takardar neman izini ta takarar kujerar sa karo na biyu a zaben 2019 karkashin sabuwar jam'iyyar ta sa.

Rashin adalci da nuna son kai na jam'iyyar APC ya sanya na sauya sheka zuwa PDP - Ayorinde

Rashin adalci da nuna son kai na jam'iyyar APC ya sanya na sauya sheka zuwa PDP - Ayorinde
Source: Depositphotos

Kazalika, 'Dan majalisar na kuma zargin jam'iyyar APC da rusa Dimokuradiyyar kasar nan sakamakon takaddamar da ta auku yayin taruka da zabukan da ta gudanar a lokutan baya.

KARANTA KUMA: Yadda na yi rashin nasara a zaben maye gurbi na jihar Bauchi - Yuguda

Ya kara da cewa, shi ya jagoranci 'yan majalisar wakilai da suka sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP sakamakon bambance-bambance na wariya gami da nuna son kai mai cike da rashin adalci na jam'iyyar APC da hakan ke barazanar zagon kasa ga Dimokuradiyya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel