2019: PDP ta tsaida dan takarar gwamna da mataimakinsa a jihar Osun

2019: PDP ta tsaida dan takarar gwamna da mataimakinsa a jihar Osun

- A shirye shiryen da take yi na fuskantar zaben 2019, jam'iyar PDP ta sanar da 'yan takarar gwamna da mataimakinsa a jihar Osun

- Jam'iyar ta ce babu ayyukan azo a gani da gwamnatin APC tayi a jihar, illa ma tarin matsalolin da ta haddasa

- PDP ta kuma yi alkawarin samar da shirye shiryen da zasu kai jihar tudun-mun-tsira

Jam'iyar PDP a jihar Osun, ta bayyana Sanata Ademola Adeleke a matsayin wanda zai tsaya takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyarta, a zaben 2019 dake gabatowa, yayin da ta tsaida Hon. Albert Abiodun Adeogun a matsayin mataimakin gwamnan.

Da ya ke bayar da wannan sanarwa ga manema labarai a babbar sakatariyar jam'iyar da ke Osogbo, shugaban jam'iyar na jiha, Soji Adagunodo, ya ce: "Wadannan sune mutanen da zasu maido da martabar jihar nan, tare da bunkasa tattalin jihar ta fannoni da dama.

"Muna masu farin cikin sanar da duniya cewa jam'iyar mu na kokarin gina kyakkyawar alaka ta taimakekeniya da wasu kusoshi a jihar Osun, don tabbatar da samun nasarar jam'iyar da kuma cire mutane daga cikin kuncin wahalar da suke ciki yanzu.

KARANTA WANNAN: Yadda amarya ta soke aurenta don mijin ya gaza tara kudin da zasuyi casu

"Jam'iyar PDP na muradin gudanar da tsaftataccen yakim neman zabe, wanda zai baiwa al'umar jihar Osun sabon yanayin rayuwa. Osun na daya daga cikin jihohi hudu da bashi yayiwa katutu a Nigeria, wanda yasa har yanzu jihar ta kasa tabuka wani abun azo a gani."

Ya kara da cewa: "Iyakar abun azo a gani da APC zata nuna a jihar Osun ba zai wuce gazawa wajen biyan ma'aikata albashi da alawus alawus ba, rashin ruwa a kowane sashe na jihar, tituna marasa kyau da kuma gine ginen gwannati marasa inganci, asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya marasa amfani, uwa uba rashin da'a a tsakanin ma'aikata, wanda ya haddasa cin hanci da rashawa.

"A bisa wannan dalili ne jam'iyar PDP ta yanke shawarar samar da shirye shirye, da zasu kai jihar dama al'uma tudun mun tsira, wanda kuma yin hakan zai dawo da martaba da bunkasa tattalin arziki na jihar."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel