Yadda na yi rashin nasara a zaben maye gurbi na jihar Bauchi - Yuguda

Yadda na yi rashin nasara a zaben maye gurbi na jihar Bauchi - Yuguda

Rahotanni dangane da zaben maye gurbi na kujerar sanatan jihar Bauchi ta Kudu sun sake bayyana yayin da tsohon gwamnan jihar, Alhaji Isa Yuguda, ya alakanta rashin nasarar sa a zaben da murda-murda gami da rashin adalci da aka gudanar.

Ko shakka babu tsohon gwamnan na daya daga cikin wadanda suka nemi takarar kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu a karkashin jam'iyyar GPN (Green Party of Nigeria), inda sakamako ya bayyana cewa ya zo a mataki na uku yayin dan takarar jam'iyyar PDP, Ladan Saliu, ya zo a mataki na biyu.

Yadda na yi rashin nasara a zaben maye gurbi na jihar Bauchi - Yuguda

Yadda na yi rashin nasara a zaben maye gurbi na jihar Bauchi - Yuguda
Source: Depositphotos

Zaben maye gurbin da aka gudanar sakamakon ajali da ya katse hanzarin mai rike da kujerar, Marigayi Isa Wakil, ya tabbatar da nasarar dan takara na jam'iyyar APC, Lawal Gumua.

KARANTA KUMA: Za a kaddamar da sabuwar Manhajar cafke 'Barayin Motoci a watan Oktoba

A yayin da yake jawabi da sanadin jagora na yakin neman zaben sa, Alhaji Abdulmumin Muhammad Kundak, Yuguda ya bayyana cewa zaben da aka gudanar cike yake da murdiya gami da rashin adalci sakamakon magudin da aka aiwatar yayin zaben.

Cikin jawaban tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa, gwamnatin jihar ta tafka magudi tare da hadin gwiwar hukumar zabe da kuma hukumomin tsaro wajen aiwatar da rashin adalci yayin zaben.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel