Abinda yasa ba zamu iya kama wadanda suka sayi kuri'a a zaben Ekiti ba - INEC

Abinda yasa ba zamu iya kama wadanda suka sayi kuri'a a zaben Ekiti ba - INEC

- Hukumar INEC ta bayar da amsa kan dalilin da yasa ba za ta iya kama wadanda ake zargin sun sayi kuri'u a zaben wasu jihohi ba

- INEC ta ce dokar kasa bai bata ikon bincika ko kama masu laifin ba face hukumomin tsaro ne suka mika mutum gare ta

- Sai dai wata kungiyar yaki da rashawa mai suna SERAP ta dau alwashin zuwa kotu don tursasawa INEC hukunta wanda ake zarginsu da sayan kuri'un

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ce ba zata iya bincika da kama 'yan siyasar da akayi ikirarin sun sayi kuri'un masu kada zabe ba a zaben gwamnan jihar Ekiti da akayi a ranar 14 ga watan Yuli saboda da izinin yin hakan a karkashin dokar kasa.

Dalilin da yasa ba za mu iya kama masu sayan kuri'u ba - INEC

Dalilin da yasa ba za mu iya kama masu sayan kuri'u ba - INEC
Source: Depositphotos

INEC ta fadi hakan ne yayin da take amsa wata wasika da kungiyar yaki da rashawa ta SERAP ta rubuta mata inda take bukatar hukumar ta gudanar da sahihiyar bincike tare da hukunta 'yan siyasan da aka ce sun sayi kuri'un masu kada zabe a Ekiti.

DUBA WANNAN: An gano wani korarren dan sanda cikin masu fashi da makami da aka cafke

A wasikar da sakataren INEC, Okechukwu Ndech ya aike wa kungiyar, ya ce INEC bata da ikon kama wani mai laifin zabe har sai hukumomin tsaro sun kama wanda ake zargin sun mika shi ga hukumar ta INEC.

INEC ta ce zata cigaba da hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin hukunta duk wanda aka samu da karya dokokin zabe.

Sai dai a martanin da SERAP ta mayar, kungiyar ta dau alwashin garzayawa kotu domin tursasa INEC da sauran hukumomin tsaro binciko wadanda ake zargi da saya kuri'u daga hannun masu zabe a Ekiti, Anambra, Edo da Ondo domin a gurfanar da su gaban kotu.

Kungiyar yaki da rashawar ta ce sayan kuri'un masu zabe ya sabawa dokar zabe kuma hakan yana sauya sakamakon zaben.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel