Dan majalisar wakilai, mambobin APC 8000 sun sauya sheka zuwa PDP

Dan majalisar wakilai, mambobin APC 8000 sun sauya sheka zuwa PDP

-Dan majalisan wakila tarayya, Mark Gbilah, ya fita daga jam’iyyar APC

-Ya bi sawun gwamnan jihar , Samuel Ortom, makoni bayan sauya shekarsa

-Ya daura laifin kisan da makiyaya ke musu ka gwamnatin tarayya

Akalla mambobin jam’iyyar All Progressives Congress, APC, tare da dan majalisar wakilai mai wakilatar mazabar Gwer West/East na jihar Benue, Mr Mark Gbilah, sun koma jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP.

Gbilah, ya jagoranci taron sauya shekar a garin Naka, hedkwatan karamar hukumar Gwer ta yamma a jiya tare da shugaban karamar hukumar, kansiloli da ma’aikatan gwamnati a yankin.

Daga cikin wadanda suka sauya sheka sune mai baiwa gwamnan jihar shawara kan al’amurorin kananan hukumomi, da babban hadimin shugaban kasa kan hulda da jama’an gari.

Yayinda yake jawabi ga jama’an, dan majalisar yace sun fita daga jam’iyyar APC bayan neman shawarwari da masu ruwa da tsaki a mazabar.

Yace: “Wannan yankin ne wanda rikicin Makiyaya yafi shafa bayan yankin Makurdi. Karamar hukumar Guma da kuma na Logo.”

“An kashe mutanenmu kuma an fitittikesu daga muhallansu amma gwamnatin tarayya tayi halin ko oho, duk da koken-koken da muka dinga yi har da gwamna Samuel Ortom.”

“Saboda hakan Mu sama da 8000 na fita daga jam’iyyar kuma da yawa na hanyar fita a kwanakin gaba yayinda jirginmu ya nufi wasu sassan mazabar da Gwer ta gabas.”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel