2019: Babu wanda zai ba Shehu Sani tikiti kai tsaye - APC

2019: Babu wanda zai ba Shehu Sani tikiti kai tsaye - APC

-Har ila yau, gaba bata kare tsakanin gwamna Nasir El-Rufa’I da Shehu Sani ba

-A makon da ya gabata, sai da El-Rufa’I ya sake tsungumar Shehu Sani a garin Birnin-gwari

-A wannan karon dai Shehu Sani bai mayar da martini ba

Sakamakon jita-jitan da ke yawo a kafofin sada ra’ayi da zumunta da kuma wasu kafafen yada labarai a kasa cewa kwamitin gudanarwan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yanke aniyar baiwa sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, tikitin kai tsaye a zaben 2019, mataimakin sakataren shirye-shiryen jam’iyyar, Muhammad Sani Ibrahim ya karyata wannan batu.

Za ku tuna cewa tun lokacin da sanata Shehu Sani ya ki sauya sheka daga jam’iyyar APC a lokacin da abokansa ke yi, sannan kuma ganawarsa da shugaba Buhari, wasu sun ahasashen cewa jam’iyyar zata fifitashi tunda gwamnan jihar yaki sulhu da shi.

KU KARANTA: Akalla mutane 1,331 hatsarin mota ya salwantar da rayuwarsu cikin watanni Uku

Mataimakin sakataren shirye-shiryen jam’iyyar, Muhammad Sani Ibrahim ya ce al’amain bada tikitin kai tsaye ya sabawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar. Ya kara da cewa sabon tsarin gudanar da zaben fidda gwani zai yi wuya a yakin Arewa maso yamma saboda yadda al’amarin siyasa yake a yankin.

Yayinda yake magana da manema labarai a karshen makon da ya gabata, Ibrahim ya jaddada cewa babu sanatan da za’a baiwa tikitin kai tsaye. Duk wanda ke da niyyar takara ya tafi zaben fidda gwani.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel