Oshiomhole ya dauki gagarumin hukunci akan gwamnonin da basu yi abun azo a gani ba ta hanyar hana su yin tazarce

Oshiomhole ya dauki gagarumin hukunci akan gwamnonin da basu yi abun azo a gani ba ta hanyar hana su yin tazarce

- Oshiomhole na yunkurin kawowa gwamnonin da basu yi kokari ba cikas

- Jihohin da ake tunanin hana gwamnoninsu tikiti kai tsaye sun hada da Kogi, Kaduna da kuma Bauchi

- Jam'iyyarna ganin wadannan jihohi basu wani taka rawar ganin da zai basu lasisin yin tazarce ba

Yayinda kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zasu gana a gobe, Alhamis, 30 ga watan Agusta, wata majiya a ranar Talata ta bayyana cewa shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole na iya rufe kofar samun tikiti kai tsaye ga wasu gwamnonin jam’iyyar da basu nuna bajinta ba.

Daga cikin gwamnonin da za’a yiwa karan tsaye sune na jihohin Kogi, Bauchi da kuma Kaduna wadanda acewar jam’iyyar basu yi wani abun azo a gani bad a zai sa har jam’iyyar ta sake tsayar da su.

A cewar majiyarmu, saboda wannan dalilin ne yasa shugaban jam’iyyar na kasa ke kokarin ganin anyi zaben fidda gwani domin zabar wadanda zasu yiwa jam’iyyar takara a zabuka masu zuwa.

Oshiomhole ya dauki gagarumin hukunci akan gwamnonin da basu yi abun azo a gani ba ta hanyar hana su yin tazarce

Oshiomhole ya dauki gagarumin hukunci akan gwamnonin da basu yi abun azo a gani ba ta hanyar hana su yin tazarce
Source: Depositphotos

A halin da ake ciki, mambobin kwamitin koli na jam'iyya mai mulki sun amince da sabon tsarin fitar da gwani na 'yan takarar su a dukkan matakai a zaben gama gari na shekarar 2019 dake a tafe

Majiyar ta mu ta Daily Trust har ila-yau ta samu cewa wannan maganar dai ta tabbata ne a daren jiya lokacin da mambobin kwamitin da suka hada da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin sa da dai sauran jiga-jigan jam'iyyar suka gana.

KU KARANTA KUMA: Abin nema ya samu: Atiku ya caccaki Buhari akan hana Kwankwaso kaddamar da takararsa

Legit.ng ta samu cewa daman dai ba tun yanzu ba, sabon shugaban jam'iyyar na kasa Kwamared Adams Oshiomhole yayi ta nanata cewa zai tabbatar da samuwar canji a yadda ake gabatar da zabukan fitar da gwani a jam'iyyar.

Sabon tsarin fitar da gwanin dai na nufin cewa dukkan wani dan jam'iyyar yana da damar a dama da shi wajen zaben 'yan takara a jam'iyyar a maimakon wakilai kawai watau 'daliget'.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel