An gano wani korarren dan sanda cikin masu fashi da makami da aka cafke

An gano wani korarren dan sanda cikin masu fashi da makami da aka cafke

- An kama wani koraren kofur din 'yan sanda, Michael Eriarebhe, da laifin fashi da makami a jihar Edo

- An gano cewa an kori Eriarebhe daga aiki ne sakamakon samunsa da laifin rashin da'a da aikata wasu laifuka

- Hukumar 'yan sandan har ila yau ta gabatar da wasu masu laifuka daban-daban da aka kama a jihar

Hukumar 'yan sanda reshen jihar Benue ta gabatar da wasu 'yan fashi da makami da aka kama ciki har da wani koraren jami'in dan sanda mai mukamin kofur, Michael Eriarebhe.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Johnson Kokumo ya ce an kori Eriarebhe daga aiki ne saboda an same shi da rashin da'a da bin dokokin aiki, kuma daga baya anyi belinsa daga kotu bayan an same shi da aikata wasu laifukan.

Dan sanda da aka kora daga aiki ya koma fashi da makami

Dan sanda da aka kora daga aiki ya koma fashi da makami
Source: Depositphotos

Kazalika, Kokumo ya janyo hankalin al'umma kan wani gidan marayu da ke Siluko Road mallakar wata mata mai suna Blessing da ake zargin ana amfani dashi wajen safarar yara. 'Yan sanda sun gano wata yarinya mai shekaru 4 da aka sace daga Legas amma daga baya aka gano ta a Edo.

DUBA WANNAN: Yadda muka shawo kan Jonathan ya amince da sakamakon zaben 2015 - Janar Abdulsalami

Sai dai, Blessing ta ce bata da masaniya cewa an sato yarinyar ne. Ta ce wani mutum da ya yi ikirarin cewa shine mahaifin yarinyar ne ya kawo ta gidan marayun kuma ta karba yarinyar ne saboda ta lura a galabaice ta ke.

Blessing ta bude gidan marayun ne shekaru hudu da suka shude da yara 15.

Shugaban 'yan sandan ya kuma bayyana cewa hukumar ta yi nasarar damke wani Sunday Onoja mai shekaru 2 da laifin kashe wani Moses Ikiri mai shekaru 27 bayan ya kai shi gonarsa a kan babur.

"Wanda ake tuhumar ya yi amfani da wani abu mai karfi wajen bugun marigayin a kai kana daga baya ya birne gawar a wata kabari mara zurfi a cikin gonar sannan ya gudu da babur din marigayin," inji Kokumo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel