Abin nema ya samu: Atiku ya caccaki Buhari akan hana Kwankwaso kaddamar da takararsa

Abin nema ya samu: Atiku ya caccaki Buhari akan hana Kwankwaso kaddamar da takararsa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya caccaka lamirin gwamnatin tarayya na hana Sanata Rabiu Musa Kwankwaso amfani da dandalin Eagle Sqaure don kaddamar da takararsa.

Legit.ng ta ruwaito Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a shafinsa na twitter, inda yace abinda gwamnatin Buhari ta yi ma Kwankwaso akan zai kaddamar da takararsa bai dace ba a tsarin Dimukradiyya.

KU KARANTA: Sauyin sheka: Wani tsohon gwamnan PDP ya jefar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda

Hakazalika Atikun yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari daya tuna lokacin da gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan bata hana shi amfani da dandalin ba da zai kaddamar da nasa takara.

“Hana Kwankwaso amfani da dandalin Eagles Sqaure bai kamata ba kwata kwata, don kuwa a ranar 15 ga watan Oktobar shekarar 2014, gwamnatin PDP ta baiwa dan takararn shugaban kasa Muhammadu Buhari izinin amfani da dandalin don kaddamar da takararsa, kuma ranar aiki ne.” Inji Atiku.

A ranar Talata, 28 ga watan Agusta ne dai hukumomin dake kula da dandalin Eagle Sqaure suka aika ma kwamitin yakin neman zaben Sanata Kwankwaso wasikar hanasu amfani da dandalin don kaddamar da takararsa ta shugaban kasa.

Wasikar ta danganta dalilin daukan wannan mataki ga cewa ranar da Kwankwaso ya shirya amfani da dandalin don kaddamar da takararsa ranar Laraba ce, kuma ranar Laraba ranar aiki ce, sai dai Sanata Kwankwaso na ganin bita da kulli kawai gwamnatin Buhari ta yi masa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel