Kotu tayi fatali da bukatar dakatar da tsige Saraki

Kotu tayi fatali da bukatar dakatar da tsige Saraki

Tun bayan ficewar Bukola Saraki daga jam'iyyar APC, ana ta tafka muhawara kan cewa ko ya cancanci ya cigaba da zama kan kujerarsa na shugabancin majalisa. Hakan yasa wasu Sanatocin PDP suka garzaya kotu don hana APC tsige Saraki amma kotun ba ta amince da hakan ba.

A jiya Talata ne wata babban kotun tarayya da ke Abuja tayi watsi da bukatar da dakatar da yunkurin da wasu 'yan majalisa keyi na tsige shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki daga kujerarsa na shugabancin majalisa.

Tun bayan sauya shekarsa daga jam'iyyar APC zuwa PDP a watan Yuli, wasu sanatoci da 'yan jam'iyyar APC suna da matsawa Saraki lamba na cewa lallai ya kamata a ajiye mukaminsa na shugabancin majalisa idan ba haka ba kuma a tsige shi da karfi.

Kotu tayi fatali da bukatar dakatar da tsige Saraki

Kotu tayi fatali da bukatar dakatar da tsige Saraki
Source: Depositphotos

A karar da Sanata Isa Missau da takwaransa Rafiu Adebayo suka shigar a kotun, sun nemi kotun ta umurci mambobin majalisar su kame daga dukkan wata yunkuri na tsige Saraki har sai lokacin da kotu da yanke hukunci kan yadda sauya shekansa zai shafi mukaminsa.

DUBA WANNAN: Ana zargin Tambuwal da yiwa Wamakko bita da kulli

Sanatocin biyu wanda suka samu wakilcin lauyoyinsu Emeka Etiaba da Mahmood Magaji sun gabatar da kararsu gaban kotu a madadin wadanda suka wakilta. Bukatarsu shine kotu ta yanke hukunci ko sauya shekan Saraki na nuna cewa dole ya sauka daga mukaminsa na shugabancin majalisa.

A yayin da yake yanke hukunci kan karar, Alkalin kotun, Nnamdi Dimgba ya ce duk da cewa bai amince da bukatar dakatar da majalisar su tsige Saraki ba, ya bukaci dukkan bangarorin biyu su guji daukan matakan da ka iya sanya shari'ar ta tambarbare.

Alkalin ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Satumban shekarar 2018.

Jam'iyyar APC sun dage kan cewa muddin Saraki bai ajiye mukaminsa da kansa ba za'a tsige shi. Sai dai a halin yanzu jam'iyyar tana da sanatoci 109 kuma wannan adadin bai kai biyu cikin uku da ake bukata kafin tsige shugaban majalisa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel