Sauran kiris: Kungiyar kwadago ta bayar da satar ansa game da karin albashi

Sauran kiris: Kungiyar kwadago ta bayar da satar ansa game da karin albashi

- Kungiyar kwadago ta bayar da satar ansa game da karin albashi

- Satakaren kungiyar ne ya bayyana hakan

- Yace kafin karshen shekarar 2018 za a fara biya

Sakataren kungunyar kwadago a Najeriya watau Nigeria Labour Congress (NLC) a turance mai suna Peter Ozo-Esan ya baiwa daukacin ma'aikatan Najeriya tabbacin cewa kafin shekarar 2018 gwamnatin tarayya zatayi karin albashi.

Sauran kiris: Kungiyar kwadago ta bayar da satar ansa game da karin albashi

Sauran kiris: Kungiyar kwadago ta bayar da satar ansa game da karin albashi
Source: Depositphotos

KU KARANTA: APC ta fitar da sabon tsarin fitar da 'yan takara a 2019

Mista Ozo-Esan ya bayar da wannan tabbacin ne a garin Abuja ranar Talatar da ta gabata lokacin da yake zantawa da kamfanin dillacin labarai inda ya ce tuni shire-shire sun yi nisa akan lamarin.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa babban dan gwagwarmayar ya ce ana sa ran kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa game da batun zai kammala rahoton sa ne a cikin farkon satin watan Satumba mai kamawa.

Daga nan kuma sai ya shawarci dukkan 'yan Najeriya da su cigaba da matsawa shugabannin gwamnatocin su a dukkan matakai domin ganin hakan ta tabbata.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta ce ta shirya tsaf domin kara gina wasu matatun mai na musamman har guda biyu a jahohin Imo da Delta dukkan su dake a kudancin Najeriya.

Kamar yadda muka samu, kamfanin albarkatun man fetur na Najeriya watau Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) shi ne ya sanar da hakan inda kuma ya kara da cewa matatun man za su rika tace akalla gangar danyen mai dubu 200 a kullum idan aka kammala su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel