Wani Bawan Allah ya sa kudi ga wadanda su ka fada masa aikin da Buhari yayi a bangaren ilmi da kiwon lafiya

Wani Bawan Allah ya sa kudi ga wadanda su ka fada masa aikin da Buhari yayi a bangaren ilmi da kiwon lafiya

Mun samu labari cewa an kalubalanci magoya bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari su fadi manyan ayyukan da Gwamnatin nan tayi wajen inganta harkar kiwon lafiya a Najeriya.

Wani Bawan Allah ya sa kudi ga wadanda su ka fada masa aikin da Buhari yayi a bangaren ilmi da kiwon lafiya

Jama'a sun kalubalanci Magoya bayan Buhari su lissafo ayyukan da aka yi a kiwon lafiya
Source: Depositphotos

Wani Bawan Allah mai suna Malam Nafiu T. ya nemi wadanda ke goyon bayan Gwamnatin Shugaban kasa Buhari su fadi wani asibiti da Gwamnatin nan ta gyara ta sa kayan aiki a cikin shekaru 3 da tayi a kan karagar mulkin Najeriya.

Har wa yau wannan Bawan Allah ya kuma nemi a fada masa wata makarantar Jami’a da Shugaba Buhari ya gyara da kayan karatu. Fiye da kwana guda kenan da wannan Bawan Allah ya aika wannan kalubale amma har yanzu shiru.

KU KARANTA: Shugaba Buhari da manyan APC su na wani taro a Villa

Kamar yadda mu ka samu labari, Nafiu yayi alkawarin zai biya N10, 000 ga duk wanda ya iya fadin Jami’ar da aka gyara ko kuma asibitin da aka kawata da kayan aiki bayan hawan Gwamnatin Jam’iyyar APC ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

A baya kun ji tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar yace Gwamnatin Buhari ba za ta iya shawo karshen matsalar talauci da tattalin arziki ba. Atiku ya kuma soki watsi da harkar lafiya da Gwamnatin Shugaba Buhari tayi a kasar.

Wani ya nemi Magoya bayan Buhari su zayyano aikin da aka yi a harkar kiwon lafiya. An kalubalanci magoya bayan Shugaban kasa Buhari su fadi aikin da aka yi a makarantu da asibitoci su samu N10, 000.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel