Tuna baya: Buhari ma a ranar aiki ya kaddamar da takarar sa a farfajiyar 'Eagle Square' a 2014

Tuna baya: Buhari ma a ranar aiki ya kaddamar da takarar sa a farfajiyar 'Eagle Square' a 2014

- Buhari ya kaddamar da taron takarar sa a Eagle Square a shekarar 2014

- Shima kuma a ranar Laraba ne ya kaddamar da takarar

- An hana Kwankwaso kaddamar da tasa takarar

Wani bincike da majiyar mu ta Daily Nigerian ta gabatar, ta bankado cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da kudurin sa na yin takara a shekarar 2014 ne a ranar Laraba kuma a farfajiyar Eagle Square.

Tuna baya: Buhari ma a ranar aiki ya kaddamar da takarar sa a farfajiyar 'Eagle Square' a 2014

Tuna baya: Buhari ma a ranar aiki ya kaddamar da takarar sa a farfajiyar 'Eagle Square' a 2014
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Ranar da Kwankwaso ya koma PDP banyi bacci ba - Ganduje

Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta hana daya daga cikin masu neman takara na jam'iyyar adawa ta PDP watau Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso filin domin kaddamar da tasa takarar.

Legit.ng ta samu cewa a da ranar Laraba 29 ga watan Agusta ne tsohon gwamnan jihar Kano ya shirya kaddamar da takarar ta sa a farfajiyar Eagle Square amma sai gwamnatin ta ce ba zata bashi wannan damar ba saboda ranar ma'aitan ta na zuwa aiki kuma hakan zai takura masu.

Sai dai al'ummomin kasar nan da dama sun yi tofin Allah-tsine game da batun inda suke ganin yin hakan tamkar muzgunawa ce ga dan takarar don yana adawa da gwamnati.

A wani labarin kuma, Mambobin kwamitin koli na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a Najeriya sun amince da sabon tsarin fitar da gwani na 'yan takarar su a dukkan matakai a zaben gama gari na shekarar 2019 dake a tafe kamar dai yadda muka samu labari daga majiyar mu.

Majiyar ta mu ta Daily Trust har ila-yau ta samu cewa wannan maganar dai ta tabbata ne a daren jiya lokacin da mambobin kwamitin da suka hada da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin sa da dai sauran jiga-jigan jam'iyyar suka gana.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel