Kada a kuskura a tsige shugaban majalisar dattawa Saraki – Inji babbar Kotun tarayya

Kada a kuskura a tsige shugaban majalisar dattawa Saraki – Inji babbar Kotun tarayya

Wata babbar kotun tarayya ta gargadi duk sanatocin dake rawan kan tsige shugaban majalisar dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki daga mukaminsa, dasu tsahirta har sai ta yanke hukunci akan karar da aka shigar gabanta, inji rahoton daily trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Alkalin kotun, mai sharia Nnamdi Dimgba ne ya sanar da haka a yayin zaman kotun na ranar Talata, 28 ga watan Agusta, inda ya bukaci a aika ma wadanda ake kara sammacin karar da aka shigar dasu.

KU KARANTA: Buhari ya sahhale ma wani Ministansa ya tsaya takarar gwamnan wannan jahar

Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya Isa Hamma Misau da na Kwara ta kudu, Sanata Rafiu Adebayo ne suka shigar da karar, inda suke nemi Kotun ta dakatar da Sanataocin APC daga tsige Saraki kamar yadda suka yi barazana biyo bayan shekewarsa daga APC zuwa PDP.

Kada a kuskura a tsige shugaban majalisar dattawa Saraki – Inji babbar Kotun tarayya

Saraki
Source: Twitter

Lauyoyin masu kara, Emeka Etiaba da Mahmud Magaji sun roki kotun ta tabbatar da tanadin sashi na 50 (2) na kundin tsarin mulkin Najweriya na shekarar 1999 dayace adadin Sanatoci 72 cikin 109 ne kadai zasu iya tsige shugaban majalisar dattawa daga mukaminsa.

Daga cikin wadanda Sanatocin suka shigar kara akwai majalisar dattawan kanta, shugaban majalisar, mataimakin shugaba, Sanata Ahmed Lawan, Sanata Bala Ibn Na Allah, Sanata Emma Buwacha, akawun majalisa da mataimakin akawun majalisa.

A jawabinsa, Alkali Dimgba yace: “Ina kira a dukkanin bangarorin dake cikin kara da su tsahirta, kuma su girmama mutuncin kotu, don haka kowa ya dauki wani mataki har sai an kammala shari’ar.” Daga karshe ya dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Satumba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel