Amurka ta bayyana matsayarta a zaben Nigeria na 2019

Amurka ta bayyana matsayarta a zaben Nigeria na 2019

- Amurka ta ce ba zata nuna bangaranci a zaben Nigeria ba don bada damar yin sahihin zabe

- Kasar ta bayyana zaben 2015 a matsayin zabe na gaskiya, wanda babu magudi a ciki

- Daga karshe kasar ta sha alwashin baiwa Nigeria duk wata gudunmawa da zata sa ayi nasara a zaben kasar dake gabatowa

Gwamnatin kasar Amurka ta ce ba zata nuna bangaranci a zaben Nigeria na 2019 dake gabatowa ba, tana mai cewa tana son wanda zai lashe zaben ya zama ya samu nasara ne ta hanyar yin sahihin zabe, wanda babu magudi ko aringizon kuri'u a ciki.

“Zamu yi iya bakin kokarinmu na tallafawa Nigeria a zabenta na 2019”, cewar jami’in hulda da jama’a, a ofishin jakadancin Amurka dake Nigeria, Aruba Amirthanayagam, a Minna, jihar Niger, a ziyarar da ya kaiwa daraktan gidan rediyon Prestige, Zubair Idris.

Aruba wanda ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta sake kaimi a zaben 2019, kamar yadda ta yi kokari a zaben 2015 da ya gabata, ya bayyana zaben 2015 a matsayin zabe na gaskiya, wanda babu magudi ko aringizon kuri’u.

KARANTA WANNAN: 2019: Cibiyar Turai ta fitar da sakamakon zaben gwaji da jin ra'ayi da ba zai yiwa PDP dadi ba

“Kasar Amurka na kyautata tsammanin zaben 2019 zai zama cikin nasara ba tare da samun magudi ba. Ina ganin zaifi kyau a maimaita irin nasarar da aka samu a zaben da ya gabata, saboda anyi zabubbuka a wasu kasashe na Afrika, kuma ba’a ji da dadi ba.” A cewar sa.

Ko da aka bukaci yayi tsokaci kan kalaman shugaban kasar Amurka Donald Trump, na kiran shugaban kasa Muhammadu Buhari “Mutum maras lakka”, a ziyarar da ya kai gidan gwamnatin Amurkan, jami’in hulda da jama’a na ofishin jakadancin Amurka ya ce: “Jaridu ne suka buga labarin, don haka su ya kamata su bada amsoshin da kuke bukata”

Jami’in ya ce ana yiwa wasu hukunce hukunce karan tsaye a kasar, wanda hakan barazana ne ga demokaradiya. Daga karshe ya kuma jinjinawa hukumar gudanarwa ta gidan Radion a kokarinsu na ganin sun gudanar da aiki bisa tsari.

Babban daraktan gidan rediyon, Idris, yay i alkawarin ci gaba da tafiyar da gidan bisa tsari da dokokin watsa labarai.

A baya Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa wani sakamakon zaben gwaji da jin ra’ayin jama’a da wata cibiyar Turai, Zeus Polls, ta gudanar ya nuna cewar jam’iyyar APC zata yi nasara a zaben 2019 tare da lashe kujerun gwamna fiye da wadanda take da su a yanzu.

Cibiyar Zeus, mai shelkwata a birnin Berlin na kasar Jamus, ta sanar da sakamakon zaben gwajin in da sakamakon zaben gwajin ya bayyana cewar duk da gunagunin da wasu ‘yan Najeriya ke yi a kan gwamnatin APC hakan ba zai hana ta samun nasarar lashe Karin wasu kujerun gwamna a zaben 2019 ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel