Sauyin sheka: Wani tsohon gwamnan PDP ya jefar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda

Sauyin sheka: Wani tsohon gwamnan PDP ya jefar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda

Tsohon gwamnan jahar Delta, kuma jigo a cikin gidan jam’iyyar PDP ya wanke kafarsa tsam ya stomata cikin gidan jam’iyyar APC, a cewarsa ya jefar da kwallon mangwaro ne domin ya samu ya huta da kuda.

Legit.ng ta ruwaito a kwanakin baya ne dai aka dinga rade radin ficewar Emmanuel Uduaghan daga PDP zuwa APC, amma taron masu ruwa da tsaki a matakin kasa na jam’iyyar APC suka yi a daren Talata ne ya raba wannan gardamar.

KU KARANTA: Takarar shugaban kasa: Kwankwaso ya sanar da sabon dandalin da zai kaddamar da takararsa a Abuja

Sauyin sheka: Wani tsohon gwamnan PDP ya jefar da kwallon mangwaro don ya huta da kuda

Uduaghan a yayin taron
Source: Depositphotos

Shi dai Uduaghan ya taba zama gwamnan jihar nan dake da tarin arzikin man fetir, jihar Delta, daga shekarar 2007 zuwa 2015, kuma ya halarci wannan taro ne daya gudana a fadar shugaban kasa, wanda shgaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Daga cikin wadanda suka halarci wannan taro akwai mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole, jagoran jam’iyyar Ahmed Bola Tinubu, tsohon shugaban APC, John Oyegun.

Sauran mutanen da aka hangi fuskokinsu a yayin taron sun hada da Gwamnonin jihohin Borno, Jigawa, Neja, Filato, Kogi, Adamawa, Ondo, Kano, Ogun, Oyo Osun, Imo, Yobe, Nassarawa, Kebbi da Legas. Hakazalika shima tsohon gwamnan jihar Borno Ali Modu Sheriff ya halarci taron.

Daga karshe Legit.ng ta ruwaito tsofaffin gwamnonin Ebonyi, Marti ELechi, Ekiti, Niyi Adebayo, Akwa Ibom, Godswill Akpabio da na Ekiti, Segun Oni, tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani da sauran ministocin gwamnatin Buhari duk sun halarci wannan muhimmin taro.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel