Sagay bai da hurumin yin magana game da zargin satifiket din Adeosun – Femi Adesina

Sagay bai da hurumin yin magana game da zargin satifiket din Adeosun – Femi Adesina

Ba sabon abu bane cewa ana zargin Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun da laifin badakalar takardar shaidar kammala bautar kasa watau NYSC na fiye da kwanaki 50 ba tare da an dauki mataki ba.

Fadar Shugaban kasa ta yi magana game da zargin ke kan wuyar Ministan ta Najeriya inda tace zargin ba laifi bane na rashin gaskiya ko kuma karbar cin hanci da rashawa. Mai magana da yawun Shugaba Buhari ne ya bayyana wannan.

Mista Femi Adesina a wani jawabi da yayi lokacin da yake magana da gidan Talabijin Channels TV a cikin kwanan nan yace ana zargin Kemi Adeosun ne da badakala ba wai maganar satar kudi ko cin amanar Gwamnatin Najeriya ba.

Hadimin Shugaban kasar ya bayyana wannan ne lokacin da yake maida amsa game da martanin da Farfesa Itse Sagay ya bada game da zargin da ke kan Ministar. Kwanaki Itse Sagay yayi watsi da zargin da ake yi wa Ministar ta kudi.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya nemi ayi masa bincike game da Adeosun

Femi Adesina dai yace tun a tashin farko Sagay bai da hurumin da zai ba Shugaban kasa shawara game da matakin da za a dauka game da Ministar domin kuwa ba bangaren aikin sa bane. Adesina yace Farfesa Sagay ya fadi ra’ayin sa ne kurum.

Farfesa Itse Sagay wanda yake ba Shugaban kasa Buhari shawara game da harkokin cin hanci yace babu dalilin sallamar Adeosun daga aiki don kurum ana zargin ta da badakalar shaidar NYSC domin kuwa ta san aikin da ta ke yi a Gwamnati.

Kalaman Itse Sagay dai sun batawa mutane da dama rai, shi dai Mai magana da yawun na Hadimin Shugaban kasar yace Sagay ya fadi ra’ayin sa ne kurum. Kwanan nan ne ma aka nada Kemi Adeosun a matsayin Shugaban Hukumar wuta na NBET.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel