2019: Wani matashi ya yi barazanar kashe kan sa idan Buhari na ci zabe ba

2019: Wani matashi ya yi barazanar kashe kan sa idan Buhari na ci zabe ba

Wani matashi a Abuja ya ja hankalin jama’a a Abuja bayan ya bayyana cewar zai kasha kan sa matukar shugaba Buhari bai ci zaben 2019 ba.

An hangi matashin wanda bai wuce shekarar 30 ba a unguwar Garki ta Abuja dauke da wata babbar fosta dake dauke da sakon zai kasha kansa idan Buhari ya fadi zabe a 2019.

Wata masoyiyar shugaba Buhari, Hadiza Bagudu, da ta yada hoton ta bayyana cewar ba zata iya kasha kanta saboda Buhari ba.

2019: Wani matashi ya yi barazanar kashe kan sa idan Buhari na ci zabe ba

Matashin da ya yi barazanar kashe kan sa idan Buhari bai ci zaben 2019 ba
Source: Facebook

Ina tafiya a unguwar Garki, Abuja, na ga wannan matashi dauke da fosta da rubutun cewar zai kasha kansa idan Buhari bai ci zaben 2019 ba,” kamar yadda Bagudu ta rubuta a shafinta na Facebook.

A wani labari na Legit.ng, kun ji cewar wani saja a hukumar ‘yan sandan Najeriya ya kashe wani mutum ta hanyar caccaka masa kwalba saboda ya ki jin gargadin da ya yi masa na ya daina neman tsohuwar matar sa.

DUBA WANNAN: Buhari, Tinubu da gwamnonin sun gana da shugabannin APC

Lamarin ya faru ne ranar Lahadi a garin Oteri dake karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta.

Sai dai an kama dan sandan, Ijeoma, tare da tafiya da shi ofishin hukumar ‘yan sanda na Patani.

An garzaya da David Ogbodo, mutumin da aka cakawa kwalbar, zuwa babban asibitin karamar hukumar Ughelli inda aka tabbatar da mutuwar sa saboda ya rasa jini mai yawan gaske.

Wasu rahotanni sun bayyana cewar auren saja Ijeoma da matar sa, Patience, ya dade da samun matsala amma tunda ba ai saki ba ya saka shi cigaba da saka ido a kan al’amuran matar tasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel