2019: Ma'aikatan jihar Nasarawa sun tsaida Agara takarar gwamnan jihar

2019: Ma'aikatan jihar Nasarawa sun tsaida Agara takarar gwamnan jihar

- Ma'aikatan jihar Nasarawa sun amince da mataimakin gwamnan jihar ya zama gwamnan su a zaben 2019

- Shugaban gamayyar kungiyoyin kwadago na jihar, ya ce sun yanke wannan hukunci ne duba da kyakkyawar alaka dake tsakanin Agara da ma'aikatan jihar

- Mataimakin gwamnan jihar, Hon. Silas Agara, ya sha alwashin bunkasa rayuwar ma'aikatan jihar idan har suka mara masa baya

Gamayyar Kungiyoyin kwadago ta jihar Nasarawa ta tsaida mataimakin gwamnan jihar, Silas Ali Agara a matsayin dan takarar su a zaben gwamnan jihar na 2019 dake gabatowa.

Shuwagabannin kungiyar sun bayyana wannan matsaya tasu ne jim kadan bayan da suka gana da mataimakin gwamnan a garin Lafia, inda shugaban kungiyar kwadago kuma shugaban gamayyar kungiyoyin ma'aikata na jihar, Comrade Abdullahi Adeka, ya zanta da manema labarai.

Ya ce sun tsaya a wannan matsaya ne kasancewar Agara mutum ne mai son ci gaban kungiyar su da kuma ma'aikatan jihar.

Adeka ya yi alkawarin hada kawunan dukkanin ma'aikatan jihar don mara baya ga Agara, wanda suke ganin ya cancanci ya shugabanci jihar, musamman ganin cewa shine dama magajin gwamnan jihar na yanzu Tanko Al-Makura.

KARANTA WANNAN: Yadda amarya ta soke aurenta don mijin ya gaza tara kudin da zasuyi casu

"Ma'aikata a jihar Nasara zasu zabi wanda yake da kishin ma'aikata da kuma kungiyoyinsu, ba wai wanda bai san ciwon ma'aikata ba" a cewarsa.

Ya yi nuni da cewa, jihar Nasarawa jiha ce da take takama da aikin gwamnati, don haka jihar zata samu gagarumin ci gaba idan har ya zamana cewa mutane irinsu Agara ne ake baiwa damar shugabantar jihar.

Tun da fari, mataimakin gwamnan jihar, Hon. Silas Ali Agara, wanda ya kira taron, ya shaidawa shuwagabannin kungiyoyin kwadagon kudirinsa na tsayawa takara, tare da bukatarsu akan mara masa baya don ganin ya samu damar sakawa ma'aikata dama wadanda suka ajiye aiki mafificin alkairi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel