Dan sandan Najeriya ya farke cikin kwarton da ya kama da matar sa

Dan sandan Najeriya ya farke cikin kwarton da ya kama da matar sa

Wani saja a hukumar ‘yan sandan Najeriya ya kashe wani mutum ta hanuar caccaka masa wuka saboda ya ki jin gargadin da ya yi masa na ya daina neman tsohuwar matar sa.

Lamarin ya faru ne ranar Lahadi a garin Oteri dake karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta. Sai dai an kama dan sandan, Ijeoma, tare da tafiya da shi ofishin hukumar ‘yan sanda na Patani.

An garzaya da David Ogbodo, mutumin da aka cakawa wukar, zuwa babban asibitin karamar hukumar Ughelli inda aka tabbatar da mutuwar sa saboda ya rasa jinni mai yawan gaske.

Wasu rahotanni sun bayyana cewar auren saja Ijeoma da matar sa, Patience, ya dade da samun matsala amma tunda ba ai saki bay a saka shi cigaba da saka ido a kan al’amuran matar tasa.

Dan sandan Najeriya ya farke cikin kwarton da ya kama da matar sa

Shugaban rundunar 'yan sanda, Ibrahim Idris
Source: Facebook

Wata makwabciyar mutumin da dan sandan ya kasha ta shaidawa jaridar Vanguard cewar saja Ijeoma tare da wasu ‘yan sanda sun zo domin kama Ogbodo tare da kai shi ofishinsu domin ya amsa tambayoyi a kan yana neman matar abokin aikin su.

DUBA WANNAN: Tsohon kwamishina ya fada komar 'yan sanda saboda laifin damfara da fashi da makami

Bayan zuwan ‘yan sandan tare da saja Ijeoma sai suka iske marigayi Ogbodo da Patience tare a dakin sa, lamarin da ya harzuka saja Ijeoma hart a kai ya dauki fasashshiyar kwalba ya caccaka wa Ogbodo din a ciki sau da yawa.

Da aka tuntubi kakakin hukumar ‘yan sanda na jihar Delta, DSP Andrew Aniamaka, ya dauki alkawarin samar da cikakken bayani a kan lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel