Dalilin da yasa na fita daga APC - Dan majalisar wakilai

Dalilin da yasa na fita daga APC - Dan majalisar wakilai

- Dan majalisa daga jihar Ondo, Ayo Ayorinde ya ce ya fice daga jam'iyyar APC ne saboda katsalandan da ake yiwa doka a jam'iyyar

- Ayorinde ya fadi hakan ne a sakatariyar PDP bayan ya sayi tikitin takarar a karkashin jam'iyyar PDP

- Dan majalisar ya ce yana daga cikin wanda suka zabi canji a baya amma daga bisani ya gamu da takaici

Dan majalisar tarayya mai wakiltan mazaban Owo/Ose ta jihar Ondo, Mr Bode Ayorinde ya ce ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP ne saboda babakere da rashin biyaya ga doka da ya zama ruwan dare a jam'iyyar.

Ayorinde ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke ganawa da manema labarai jim kadan bayan ya sayi tikitin takarar gwamna a sakatariyar jam'iyyar PDP da ke Akure a yau Talata.

Dalilin da yasa na fice daga jam'iyyar APC - Dan majalisar wakilai Ayorinde

Dalilin da yasa na fice daga jam'iyyar APC - Dan majalisar wakilai Ayorinde
Source: Depositphotos

Idan mai karatu bai manta ba, Ayorinde yana daya daga cikin 'yan majalisar wakilai da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a ranar 24 ga watan Yulin wannan shekarar.

DUBA WANNAN: Ana zargin Tambuwal da yiwa Wamakko bita da kulli

Kazalika, dan majalisar ya ce jam'iyyar APC ta bawa masu kishin demokradiya kunya a babban taron ta na kasa da tayi a wannan shekarar.

"Wannan ba shine irin canjin da muke zaba ba. Nayi yakin neman zabe domin a samu canji amma a yanzu ina cike da takaici game da yaddda APC ke gudanar da mulki.

"Na koma jam'iyyar PDP ne saboda in karfafa jam'iyyar tare da karfafa demokradiya da kawo cigaba a Najeriya," inji Ayorinde.

A jawabin da ya yi, Ciyaman din PDP na jihar Ondo, Mr Clement Faboyede ya yi maraba da Ayorinde kuma ya tabbatar masa cewa ba za'a nuna masa banbanci ko tsangwama a jam'iyyar ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel