Buhari ya sahhale ma wani Ministansa ya tsaya takarar gwamnan wannan jahar

Buhari ya sahhale ma wani Ministansa ya tsaya takarar gwamnan wannan jahar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince ma ministan sadarwar, Adebayo Shittu ya tsaya takarar gwamnan jihar Oyo a zaben shekarar 2019, Buhari ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Talata, 28 ga watan Agusta a garin Ibadan.

Legit.ng ta ruwaito wannan wasikar ta zamto raba gardama game da hasashen da ake yin a ko Minista Shittu zai tsaya takarar gwamna ko a’a, musamman duba da tsatstsamar dangantakar dake tsakaninsa da gwamnan jihar, Abiola Ajimobi.

KU KARANTA: Gwamnati ta hana Kwankwaso dandalin daya shirya kaddamar da takararsa a ciki

Cikin wasikar daya aika ma Minista Shittu, Buhari yace: “Na samu wasikar daka aiko min inda kake bayyana burinka na tsayawa takarar gwamnan jihar Oyo a zaben shekarar 2019, da farko dai ina gode ma a madadin majalisar zartarwa da yan Najeriya bisa ayyukan da ka yi a matsayinka na minista.

Buhari ya sahhale ma wani Ministansa ya tsaya takarar gwamnan wannan jahar

Shittu
Source: Depositphotos

“Ina sane da gudunmuwar daka bayar a baya ga jam’iyyar APC, musamman a gabanin zaben 2015, da kuma bayanta, kamar yadda ka sani ne, bani da wata bukatar data wuce a gudanar da zaben gaskiya da gaskiya, kuma ina goyon bayan dukkanin yan takarkarun APC, kaima ina maka fatan alheri.” Inji Buhari.

Tuni minista Shittu ya kaddamar da takararsa ta mukamin gwamnan jihar tare da fara yakin neman zabe, shittu haifaffen garin Saki ne, kuma ya taba zama dan majalisar dokokin jiha mai wakiltar Saki, sa’annan yayi kwamishina har sau biyu.

Ana sa ran nan bada jimawa ba ministan zai yi murabus daga mukaminsa na minista don tunkarar yakin neman zaben ansa gadan gadan, wannan ne ya kawo adadin yan takarar gwamnan jihar Oyo a APC zuwa goma sha hudu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel