'Yan sanda sun yi ram da kayan sojoji a wata jihar Kudu

'Yan sanda sun yi ram da kayan sojoji a wata jihar Kudu

A yau Talata ne hukumar 'yan sanda reshen jihar Abia ta sanar da cewa ta gano wasu kayaykin soji masu dimbin yawa a wata dakin ajiyar kayayaki a garin Aba da ake kyautata zaton an sayo daga kasar China ne.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Anthony Ogbizi ne ya bayar da sanarwan a Umuahia yayin da yake yiwa manema labarai a kan nasorin da rundunar ta samu wajen yaki da masu aikata laifuka cikin makonni biyu da suka wuce.

Mr Ogbizi ya ce tuni an kama mai dakin ajiyar kayayakin, Michael Onuoha bisa laifin hadin baki da taimakawa masu aikata laifi da sayan haramtatun kayayaki wanda galibinsu tufafi ne irin na sojin Najeriya.

An kama dandazon kayayakin soji da aka shigo da su ta barauniyar hanya

An kama dandazon kayayakin soji da aka shigo da su ta barauniyar hanya
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An gurfanar da tsohon kwamishina a kotu bisa zargin sata da damfara

Ya yi ikirarin cewa babban manajan kamfani U.U. Iruoha mai suna Uche Iruoha wanda akafi sani da Urchman ne ya yi odar kayayakin a cikin wata kwantena da aka dauka daga Apapa Legas zuwa garin Aba a watan Maris.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce an kama Mr Onuoha a ranar 16 ga watan Augusta amma Mr Iruoha har yanzu yana kasar China.

Kwamandan Brigade na 14 na sojin Najeriya, Abubakar Ibrahim wanda ya hallarci taron tare da kwamishinan 'yan sandan ya ce hukumar sojin ta na mtukar damuwa kan afkuwar irin wannan lamarin. Ibrahim ya ce babu shakka wasu bata gari ne ke amfani da kayayakin sojin wajen aikata miyagun ayyuka da sunan sojin Najeriya.

Ya ce hukumar sojin za ta cigaba da hadin gwiwa da hukumar 'yan sanda da sauran jami'an tsaro domin magance matsalar tare da tabbatar da cewa an kama tare da hukunta dukkan masu hannu cikin lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel