Bianca Ojukwu ta ƙaddamar yaƙin neman zaben Kujerar Sanata a yau Talata

Bianca Ojukwu ta ƙaddamar yaƙin neman zaben Kujerar Sanata a yau Talata

Mun samu cewa Ambasada Bianca Ojukwu, uwargidan marigayi shugaban kabilar Ibo, Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, ta ƙaddamar da yaƙin neman zaben kujerar Sanata ta Kudancin jihar Anambra a ranar yau ta Talata.

Za a gudanar da wannan taro na ƙaddamar da ƙudirin Uwargidan marigayi Ojukwu a farfajiyar wasanni ta Ekwulobia dake karamar hukumar Aguata ta jihar kamar yadda shafin jaridar The nation ya ruwaito.

Bianca wadda tsohuwar jakadan Najeriya ce zuwa kasar Andalus, za ta nemi takarar kujerar Sanata karkashin jam'iyyar APGA (All Progressive Grand Alliance), inda Marigayi Ojukwu ya shafe fiye da shekaru 10 yana neman kujerar shugaban kasa ba tare da samun nasara ba.

Bianca Ojukwu ta fara yaƙin neman zaben Kujerar Sanata a yau Talata

Bianca Ojukwu ta fara yaƙin neman zaben Kujerar Sanata a yau Talata
Source: Depositphotos

Kazalika Bianca za ta fafata takarar kujerar Sanatan da wasu hamshakan 'yan kasuwa; Ifeanyi Uba da kuma Nicholas Ukachukwu a zaben fidda gwani na jam'iyyar da za a gudanar a kwana-kwanan nan.

KARANTA KUMA: Kasafin Kudi Zabe: Majalisar Dokoki ta yi na'am da buƙatar shugaba Buhari ta N143bn

Bincike ya bayyana cewa, akwai yiyuwar Bianca na neman fafata takarar ta a karkashin jam'iyyar APGA a sakamakon gudunmuwa gami da gwagwarmaya da Marigayi maigidanta yayi wajen kafuwar ta.

A yayin da yake jawabi dangane da kudirin Bianca, wani fitaccen attajiri, Dakta Godwin Maduka, ya bayyana cewa wannan kudiri wani tabarraki ne ga mazabar Kudancin jihar Anambra.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel