Ke duniya: Ya kashe dan Achaba, ya binne gawarsa a asirce

Ke duniya: Ya kashe dan Achaba, ya binne gawarsa a asirce

Wata Kotun majistri dake gari Ado-Ekiti ta daure wani manomi mai suna Toyin Ajakaye sakamakon tuhumarsa da ake yi da zargin kashe wani dan Achaba, Omoniyi Are biyo bayan fada daya kaure a tsakaninsu akan kudin da zai biya dan Achabar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Toyin ya aikata wannan kisa ne a ranar 22 ga watan Agusta a garin Agbado-Ekiti dake karamar hukumar Gbonyan. Toyin ya shaida ma Kotun cewa rikici ne ya kaure tsakaninsa da dan Achanar akan kudin daya nemi ya biyashi.

KU KARANTA: Gwamnati ta hana Kwankwaso dandalin daya shirya kaddamar da takararsa a ciki

“Dan Achaban ya daukoni ne daga cikin gari zuwa gonata, kuma ya nemi na biya shi N200, ni kuma nace ba zan biyashi ba, sai dai N100, daga nan fa sai muka cacar baki, ni kuma na shake masa wuya, yayin da yayi kokarin kama min mazakuta, a haka ne ya mutu.” Inji shi.

Sai dai manomin yace daya fahimci ba zai iya daukan gawar dan achabar bane sai ya hara rami ya binne shi, amma Allah ya tona asirinsa a lokacin da wasu jama’a suka hangeshi, inda suka kama shi.

Sai dai Dansanda mai kara ya musanta bayanan manomin, inda yace shake wuyar dan achabar yayi da igiya, kuma ya binne shi a boye, ya kara da cewa bincikensu ya nuna an taba kama manomin da laifin satan bunsuru, don haka basu yi mamakin abinda ya aikata ba.

Daga bisani Dansanda mai kara ya roki Kotu ta daure wanda ake kara, yayin da lauyan wanda ake kara ya nemi Kotun ta mayar da karar ga ma’aikatan shari’a zuwa lokacin da zai nemi belin wanda yake karewa.

Bayan sauran bangarorin biyu, Alkalin kotun Modupe Afeniforo ta dage karar zuwa ranar 16 ga watan Oktoba, sa’annan ta bada umarnin garkame mata wanda ake kara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel