'Yan bindiga sun bindige tsohon kansila a Delta

'Yan bindiga sun bindige tsohon kansila a Delta

A jiya Litinin ne wasu 'yan bindiga suka bindige tsohon kansila a karamar hukumar Ughelli ta Kudu da ke jihar Delta mai suna Blessing Oguori.

Kwamsihinan 'yan sanda na jihar Delta, Mustapha Muhammad ya tabbatar da afkuwar lamarin a wata hira da ya yi da manema labarai a Warri kamar yadda Premium Times ta wallafa.

Mr Mustapha ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin a layin Osubi da ke karamar hukumar Okpe da ke jihar ta Delta.

'Yan bindiga sun bindige tsohon kansila a kudancin Najeriya

'Yan bindiga sun bindige tsohon kansila a kudancin Najeriya
Source: Depositphotos

Ya ce tuni hukumar ta fara gudanar da bincike inda ya kara da cewa, "jami'an mu sun bazama neman wadanda suka aikata kisar domin an san ko su wanene ne".

DUBA WANNAN: An gurfanar da tsohon kwamishina a kotu bisa zargin sata da damfara

Wadanda abin ya faru a idanunsu sun ce marigayin yana tare da dansa, Newton Agbofodo wanda shima 'yan bindigan sun harbe shi amma bai mutu ba.

"Oguori tsohon mataimakin Agbofodo ne kuma yana tare da yaron tsohon mai gidansa ne wanda shima 'yan bindigan sun harbe shi amma ba ta ratsa shi," inji wani da akayi harbi a idanunsa.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce an ajiye gawar Mr Oguori a dakin ajiyar gawa na wata asibiti da bai ambace sunan ta ba kamar yadda kamfanin dillanci labarai (NAN) ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel