Kada Donald Trump ya halarci jana’iza ta – Wasiyyar John McCain

Kada Donald Trump ya halarci jana’iza ta – Wasiyyar John McCain

Marigayi Sanata John McCain ya haramtawa shugaban kasan Amurka Donald Trump halartan jana’izarsa a wasiyyar da ya bari. An bukaci tsohon shugaban kasa Barack Obama da George Bush suyi jawabi a jana’izar tsohon dan takaran shugaban kasar Amurkan.

John McCain wanda ya mutu ranan Asabar, 26 ga watan Agusta 2018, ya bukaci tsaffin shugabannin kasan suyi jawabi a jana’izar da za’a gudanar ranan Asabar a cocin Washington’National Cathedral, game da cewar CBS News.

Rahoton ya bayyana cewa shugaban kasan Amurka Donald Trump ba zai halarci taron ba bisa ga wasiyyar marigayin kafin mutuwarsa.

Kada Donald Trump ya halarci jana’iza ta – Wasiyyar John McCain

Kada Donald Trump ya halarci jana’iza ta – Wasiyyar John McCain
Source: Twitter

An sanar da fadar shugaban kasa Amurkan bukatar John McCain tun kafin mutuwarsa, amma mataimkain shugaban kasam, Mike Pence zai halarta.

Obama da Bush sun kayar da Mc Cain a takarar kujeran shugabancin kasar. Yayinda Bush ya kayar da shi a shekarar 2000, Obama ya kayar da shi a shekarar 2008. Amma suna ganin mutuncin juna.

Obama ya siffanta Mc Cain a matsayin wanda ya sadaukar kansa wajen fifita kasar akan kansa.

Sanata John McCain ya mutu watanni alanta cewa yana fama da cutar daji na kwakwalwa a shekarar 2017. Ya mutu yana dan shekara 81 a duniya. Ya kasance dan majalisar dattawan kasar har mutuwarsa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel