Kasafin Kudi Zabe: Majalisar Dokoki ta yi na'am da buƙatar shugaba Buhari ta N143bn

Kasafin Kudi Zabe: Majalisar Dokoki ta yi na'am da buƙatar shugaba Buhari ta N143bn

Mun samu cewa, kwamitin majalisar dokoki ta tarayya akan al'amurran hukumar zabe ta kasa watau INEC, ta bayar da sahalewar ta kan bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta tanadar N143bn domin gudanar da babban zabe na 2019.

Majalisar ta yi na'am da bukatar ta shugaba Buhari yayin wata ganarwar sirrance da kwamitin ya gudanar cikin birnin Abuja a ranar Litinin din da ta gabata.

Kwamitin ya hadar da Sanatoci da 'yan majalisar wakilai inda suka amince da bukatar ta shugaban kasa yayin zaman da suka gudanar cikin babban birnin na tarayya.

Kasafin Kudi Zabe: Majalisar Dokoki ta yi na'am da buƙatar shugaba Buhari ta N143bn

Kasafin Kudi Zabe: Majalisar Dokoki ta yi na'am da buƙatar shugaba Buhari ta N143bn
Source: Depositphotos

Rahotanni sun bayyana cewa, mambobin majalisar sun tafka muhawara kan amincewa da kasafin kudin zabe na N189bn ko kuma tanadar wani kaso na N143bn daga cikin kasafin kudin kasa na 2018 kamar yadda shugaban kasar ya bukata.

KARANTA KUMA: Buhari ba zai iya haɓaka tattalin arzikin kasar nan ba - Kwankwaso

Shugaban kwamitin, Sanata Suleiman Nazif, shine ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai bayan zaman majalisar da suka gudanar, inda ya ce sun amince da bukatar shugaba Buhari na tanadar N143bn cikin kasafin kudin 2018 domin gudanar da zaben 2019 .

Legit.ng ta fahimci cewa, a ranar 17 ga watan Yulin da ya gabata shugaba Buhari ya bayyana wannan bukata cikin wata rubutacciyar wasika ga majalisar dokoki tarayya, inda shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya yi fashin baki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel