Allah ne ya aiko Buhari don ya ceci Najeriya - Gwamnan APC

Allah ne ya aiko Buhari don ya ceci Najeriya - Gwamnan APC

- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana dalilin da yasa 'yan Najeriya zasu sake shugaba Buhari a zaben 2019

- Bello ya bayyana cewar Allah ne ya turo Buhari domin ya ceci Najeriya daga bakin mulki irin na masu kama-karya

- Gwamnan ya bukaci matasa da su daina bari 'yan siyasa marasa kishi na amfani da su domin bangar siyasa

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bukaci 'yan Najeriya su goyawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a yunkurinsa na ganin ya sake lashe zabe a karo na biyu.

Gidan Talabijin na Channels ya rawaito cewar gwamna Bello na wadannan kalamai ne yayin bude wani babbab masallaci a jiya, Litinin, 27 ga watan Agusta, a garin Okene tare da shaidawa jama'a cewar Allah ne ya aiko Buhari domin ya ceci Najeriya daga bakin mulki irin na masu kama-karya.

Allah ne ya aiko Buhari don ya ceci Najeriya - Gwamnan APC

Shugaba Buhari
Source: Twitter

Kazalika, gwamnan ya shaidawa jama'ar da suka halarci taron bude masallacin cewar gwamnatinsa zata cika dukkan alkawuran da ta daukarwa jama'ar jihar kafin ya hau mulki.

"Ya kamata mu hada kai domin goyon bayan shugaba Buhari, mutumin da Allah ya aiko domin ceton Najeriya daga hannun azzaluman shugabanni.

DUBA WANNAN: 2019: PDP ta zayyana zunuban Buhari da zasu kayar da shi zabe

"Mu bawa shugaba Buhari hadin kai da kuma gwamnatin jihar Kogi wacce ke iya bakin kokarinta domin ganin ta kyautata rayuwar mutanenta," a cewar gwamna Bello.

A cikin dogon jawabin da gwamnan ya gabatar, ya yi kira ga matasa da su daina bari 'yan siyasa marasa kishi na amfanin da su wajen bangar siyasa ko aiyukan daba lokacin zabe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel