Buhari ba zai iya haɓaka tattalin arzikin kasar nan ba - Kwankwaso

Buhari ba zai iya haɓaka tattalin arzikin kasar nan ba - Kwankwaso

A ranar Ltinin din da ta gabata ne tsohon gwamnan jihar Kano kuma manemin takarar kujerar shugaban kasa a jam'iyyar adawa ta PDP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya kwancewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zani a kasuwa dangane da yadda yake tafi da al'amurran bunkasa tattalin arzikin kasar nan.

Tsohon gwamnan ya kuma bayyana takaicin sa dangane da yadda gwamnatin shugaba Buhari ta gaza wajen inganta ci gaban gine-gine a yankunan Kudu maso Gabashin kasar nan, inda ya yi kira akan sauya gwamnatin yayin zaben 2019.

Sanatan ya bayyana hakan ne ga mambobin jam'iyyar su ta PDP a babban birnin Owerri na jihar Imo, a yayin da ya ke ci gaba tuntube-tuntunbe gami da shawagin neman amincewar al'ummar kasar nan wajen mara masa baya a zaben 2019.

Buhari ba zai iya haɓaka tattalin arzikin kasar nan ba - Kwankwaso

Buhari ba zai iya haɓaka tattalin arzikin kasar nan ba - Kwankwaso
Source: Twitter

Kwankwaso yake cewa, dukkanin wadanda suka fice daga jam'iyyar PDP a shekarar 2014 domin goyon bayan kudirin shugaba Buhari na kujerar shugaban kasa, su na da nasani a halin yanzu sakamakon gazawar sa musamman ta fuskar tattalin arziki da kuma halin da kasar nan take ci a yanzu.

KARANTA KUMA: Ana neman harzuƙa rikicin Makiyaya da Manoma a jihar Filato

Tsohon Ministan ya kuma bayyana fatansa gami da sa ran jam'iyyar ta PDP za ta karbi ragamar mulkin tare kafa gwamnati cikin jihohi da dama na kasar nan a shekara mai gabatowa.

Kwankwaso ya kara da cewa, mafi akasarin al'ummar kasar nan sun kai makura ta fuskar gajiya da mulkin kama karya na jam'iyyar APC, inda suke fata tare da kusanto farin ciki yayin da jam'iyyar PDP ta karbi mulki a kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel