Shehu Sani ya caccaki Trump kan furucin da yayi game da Buhari

Shehu Sani ya caccaki Trump kan furucin da yayi game da Buhari

- Sanata Shehu Sani yayi Allah wadai da furucin Trump akan Buhari

- Ya kalubalanci shugabannin Afrika da su cire tsoro su kare martabarsu

- Sani ya shawarce su da su daina neman yaddan kasashen waje a fannin siyasa da tattalin arziki

Sanata Shehu Sani mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin kasar yayi Allah wadai da mumunan furucin da Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayi akan Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari.

Jaridar Financial Times (FT) dai ta rahoto cewa Mista Trump ya bayyana Shugaba Buhari a matsayin mara kuzari bayan ganawarsu a watan Afrilu.

Trump ne ya gayyaci Buhari zuwa Washington a ranar 30 ga watan Afrilu yayinda shugabannin biyu suka tattauna lamura ciki hadda yaki da ta’addanci da sauran barazanar tsaro da zaman lafiya.

Shehu Sani ya caccaki Trump kan furucin da yayi game da Buhari

Shehu Sani ya caccaki Trump kan furucin da yayi game da Buhari
Source: Depositphotos

An tattaro cewa Trump yace baya fatan sake ganawa da Shugaban kasar domin ya kasance tamkar “gawa”.

Da yake mayar da martani akan haka, Shehu Sani yace furucin “kamar sauran lokuta Mista Trump ya sha maganganun batanci akan Afrika, hakan hari ne ga Najeriya da nahiyar.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama wasu ma’aurata masu tabbin hankali dauke da sassan jikin dan Adam a Lagas

Ya kalubalanci shugabannin Afrika das u kare martabarsu yayinda ya umurce su da su ne ci gaban siyasa da tattalin arziki a tsakanin nahiyarsu maimakon fita waje.

Ya kuma yi Allah wadai da Kalmar gawa da Trump ya furta akan Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel