Sojojin da suka bore a filin jirgin saman Maiduguri sun shiga uku, za’a gurfanar da su

Sojojin da suka bore a filin jirgin saman Maiduguri sun shiga uku, za’a gurfanar da su

Hukumar sojin Najeriya ta ce zata shirya kotun soji GCM domin gurfanar da jami’an sojin da suka gudanar da zanga-zanga a filin jirgin saman Maidugri, jihar Borno, makonni biyu da suka gabata.

Wannan sanarwa ya biyo bayan gargadin da hukumar sojin tayi cewa ba za ta lamunci rashin da’a da tarbiyya daga jami’anta da hafsoshinta ba ko ma me ya faru. Saboda haka ya saba dokoki da ka’idar gidan Soja kuma duk wanda aka kama da hakan zai fuskanci fushi doka.

Ta bayyana hakan ga sojin musamman masu yaki da ta’addanci a Arewa masa gabashin Najeriya.

Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Abbah Dikko, ya sanar da wannan gargadi ne yayinda kaddamar da cibiyar soji a Maiduguri karshen makon da ya gabata.

KU KARANTA: Nan gaba kadan zamu bayyana matsayinmu kan Leah Sharibu - Fadar Shugaban kasa

Dikko, wanda yayi Allah wadai da wannan zanga-zanga da wasu jami’a soji sukayi ta hanyar harbin bindiga a filin jirgin sama saboda an mayar da su wata karamar hukumar a jihar. Ya tunawa sojojin alkawarin da sukayi yayinda suka shigo gidan soja.

Dikko Yace: “Da kanku kuka yanke shawaran sadaukar d rayukanku don kare mutuncin Najeriya. Saboda haka yanada muhimmanci mun tuna hakkokinmu ga kasa."

“Wadanda suka sadaukar da kansu domin bautawa Najeriya, hakkin hukuma ne ta tura ku duk inda taga kun dace da wajen.”

Ya karashe jawabinsa da cewa yana da muhimmanci su fahimci cewa wannan bauta ne ga kasarsu ba kansu ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel