Za'a duba lafiyar yara da mata masu juna biyu guda 1.6 miliyan kyauta a jihar Bauchi

Za'a duba lafiyar yara da mata masu juna biyu guda 1.6 miliyan kyauta a jihar Bauchi

- Kananan yara yan kasa da shekaru 5 da mata masu juna biyu zasu samu tallafin kiwon lafiya da abinci mai gina jiki kyauta a jihar Bauchi.

- Uwar gidan gwamnan jihar, Hajiya Hadiza Mohammed Abubakar ce ta sanar da hakan a wani shirin bunkasa rayuwar jarirai

- Shirin bada tallafin kiwon lafiyar nada hadin guiwa da gwamnatin jihar da wasu kungiyoyin sa kai na kasashen waje.

Uwar gidan gwamnan jihar Bauchi Hajiya Hadiza Mohammed Abubakar, ta bayyana cewa akalla kananan yara Miliyan 1.3 da mata masu juna biyu 300,000 ne ake sa ran zasu amfana da wani shirin bada kiwon lafiya da abinci kyauta a jihar Bauchi.

Ta bayyana hakan ne a wani taro na kaddamar da bikin satin bunkasa rayuwar jarirai da mata masu juna biyu MNCH na wannan shekarar a Bauchi.

Da take jawabi a wajen taron da ya gudana a cibiyar kiwon lafiya dake Yelwa, kwaryar Bauchi, Hajiya Hadiza Abubakar ta ce an shirya bikin satin MNCH don bunkasa lafiyar jarirai da samar da abinci mai gina jiki ga mata masu dauke da juna biyu.

Misis Abubakar ta bayyana cewa hukumar lafiya ta duniya WHO tare da hadin guiwar majalisar zartaswa kan lafiya ta duniya ne suka amince da gudanar da bikin satin a kowace shekara, wanda kuma yake samun tallafi daga kungiyoyi irinsu UNICEF.

KARANTA WANNAN: Yadda amarya ta soke aurenta don mijin ya gaza tara kudin da zasuyi casu

Ta ce bada tallafin kiwon lafiya kyauta zai shafi kananan yara da mata masu juna biyu, wanda yanhada da gwaji da bada magunguna da kuma sinadaren gina jiki.

"Abubuwan da za'a raba sun hada da sinadaran Vitamin A, rigakafi, ruwa mai gina jiki da dai sauransu, don rage tamowa a tsakanin kananan yara yan kasa da shekaru biyar, da kuma rage kamuwa da cutar gudanawa, kyanda da sauransu

"Har ila yau a cikin bikin wannan satin, zamu wayarwa mata kai dangane da muhimman yin wasu aikace aikace a cikin gida, wanda zai kaiga bunkasa lafiyarsu." A cewar ta.

Don haka matar gwamnan ta bukaci mata masu dauke da juna biyu, da kuma iyaye masu yara yan kasa da shekaru biyar, da su tura su zuwa ga cibiyoyin kiwon lafiya mafi kusa, don amfana da wannan tallafi.

Tun farko, da ya ke jawabi, shygaban hukumar ilimi a matakin farko na jihar, Famasi Adamu Ibrahim Gamawa ya ce za'a gudanar da shirin bada tallafin kiwon lafiyar a cibiyoyin kiwom lafiya 323 dake a fadin jihar, da kuma manyan cibiyoyin kiwon lafiya guda biyu dake kowace gunduma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel