Ana zargin Tambuwal da yiwa Wamakko bita da kulli

Ana zargin Tambuwal da yiwa Wamakko bita da kulli

- Ana tuhumar gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato da yin barazana ga Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko

- Wannan ya biyo bayan harin da wasu 'yan daba da ake zargin suna yiwa Tambuwal aiki ne suka kaiwa Wamakko kan hanyarsa ta zuwa filin tashin jiragen sama

- Har yanzu, gwamna Aminu Waziri Tambuwal bai yi tir da harin da aka kaiwa Wamakko ba

Abubuwan da ke faruwa a jihar Sakkwato na nuni ga cewa gwamna jihar ya fara amfani da 'yan daba wajen yin barazana ga shugabanin jam'iyyar APC a jihar saboda basu goyi bayansa ba a yayin da sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Daya daga cikin wadanda ake yiwa wannan barazanar shine tsohon gwamnan jihar, Sanata Aliyu Magatarda Wamakko da 'yan daba da ke yiwa gwamna Tambuwal suka kaiwa hari kamar yadda wani rahoto da Leadership ta wallafa ya ce.

An zargin Tambuwal da yiwa Wammako bita da kulli

An zargin Tambuwal da yiwa Wammako bita da kulli
Source: Twitter

Harin na farko ya faru ne a kwana-kwanan nan inda wasu 'yan daba da ake zargin suna yiwa gwamna Tambuwal aiki su kayi kwanciyar bauna suka kaiwa Magatakarda Wamakko hari a hanyarsa ta zuwa filin tashin jirage na Sultan Abubakar.

DUBA WANNAN: 2019: Dan takarar PDP ya yi tsokaci kan farin jini Buhari a arewa

Barazanar na biyu ta faru ne kwanakin baya a lokacin da wasu 'yan daba da ake kyautata zaton an dauki hayansu ne suka fito titunan garin Goronyo suna zanga-zangar cewa Magatakarda Wamakko bai taba tsinana musu komai a yankin ba lokacin da ya ke gwamna.

Duk wani mai bibiyar siyasar jihar Sakkwato zai iya fahimtar cewa akwai wata bita da kulli da ake shiryawa duba da cewa Wamakko ya sauka daga mulki tun shekaru uku da suke shude a 2015. Wani abin mamaki kuma shine gwamnatin jihar mai mulki yanzu bata fito tayi Allah wadai da harin da aka kaiwa Wamakko ba.

Wasu maso nazarin lamuran yau da kullum a jihar Sakkwato sun shawarci gwamna Tambuwal ya dena huce fushinsa a kan abokan adawa bisa matakin da ya dauka na komawa jam'iyyar PDP saboda yana son ya yi takara da shugaba Muhammadu Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel