Ana neman harzuƙa rikicin Makiyaya da Manoma a jihar Filato

Ana neman harzuƙa rikicin Makiyaya da Manoma a jihar Filato

Mun samu cewa dimuwa gami da tashin hankali na neman aukuwa a jihar Filato yayin da masu adawa da kuma kishin zaman lafiya ke yunkurin kulla makirci na harzuƙa rikicin makiyaya da manoma a jihar.

Wannan kullalliya wani shiri na yunkurin katse walwala gami da jin dadin zaman lafiya da kwanciyar hankali da ta wanzu a jihar kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan kungiya mai adawa da zaman lafiya na da hannu na sanadiyar hare-haren da suka auku a kwana-kwanan nan cikin wasu kauyuka a makonnin da suka gabata.

Legit.ng ta fahimci cewa, daya daga cikin hare-haren da suka auku shine na wani mutum, Hawal Shuaibu, a kauyen Dorawa yayin da ya fidda shanun sa kiwo a ranar Litinin din da ta gabata.

Ana neman harzuƙa rikicin Makiyaya da Manoma a jihar Filato

Ana neman harzuƙa rikicin Makiyaya da Manoma a jihar Filato
Source: Facebook

Maharan rike da bindigu sun harbe Mallam Hawal inda kuma suka yi awon gaba da shanun sa kimanin 100 yayin da ya yi shame-shame rai a hannun Mahaliccin sa.

Sai dai a halin yanzu, hukumomin tsaro sun yi tsayuwar daka wajen ganin bayan wannan mamuganta masu yaki da zaman lafiyar da kwanciyar hankalin al'umma a jihar.

KARANTA KUMA: Ba sauya fasalin 'Kasa ne matsalar Najeriya ba - Osinbajo

Wata majiyar rahoto ta bayyana cewa, ko shakka babu bincike irin na leken asiri ya tabbatar da cewa, ana kulla makircin kai hari kan makiyaya na Fulani tare da dabbobin su na kiwo domin harzuƙa rikici a tsakanin su da Manoma musamman a yankunan Berom na jihar ta Filato.

Majiyar ta kara da cewa, akwai mamaki dangane da yadda gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta samar da zaman lafiya a Arewa ta Tsakiya da kuma wasu yankun Arewa maso Yammacin kasar nan musamman jihar Zamfara da kuma babbar hanyar garin Birnin Gwari dake jihar Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel