Abinda yasa ba zan iya amsa gayyatar 'yan sanda ba - Fani-Kayode

Abinda yasa ba zan iya amsa gayyatar 'yan sanda ba - Fani-Kayode

- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya bukaci hukumar 'yan sanda ta dage ranar da zai amsa gayyatar da tayi masa

- 'Yan sandan sun gayyaci Fani-Kayode ne a gurfana a ranar 28 ga watan Augusta bisa zarginsa da wallafa rubutun da ka iya hadasa fitina

- Fani-Kayode ya ce ba zai samu amsa gayytar a ranar ba saboda akwai wata muhimmiyar taro da ya shirya hallarta

Tsohon ministan sufurin jiragen sama na kasa, Cif Femi Fani-Kayode ya rubuta wasika ga hukumar 'yan sandan Najeriya inda ya yi bayyanin dalilan da yasa ba zai samu ikon amsa gayyatar da aka yi masa a yanzu ba.

A makon da ta gabata, hukumar 'yan sanda ta gayyaci Fani-Kayode bisa zarginsa da wallafa wani rubuta mai alaka da tayar da fitina tsakanin jama'a inda ta bukaci ya bayyana a gabanta kafin ko ranar 28 ga watan Augustan wannan shekarar.

Abinda yasa ba zan iya amsa gayyatar 'yan sanda ba - Fani-Kayode

Abinda yasa ba zan iya amsa gayyatar 'yan sanda ba - Fani-Kayode

Sai dai a wasikar da ya aike mai dauke da sa hannun lauyansa, Mr Kayode Ajulo, Fani Kayode ya ce ba zai samu amsa gayyatar 'yan sandan ba saboda zai hallarci babban taron kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) wanda za'a gudanar a ranar Talata a Abuja.

DUBA WANNAN: An gurfanar da tsohon kwamishina a kotu bisa zargin sata da damfara

Wani sashi na wasikar ya ce, "Wanda muke karewa yana bukatar a dage ranar da zai bayyana zuwa ranakun 4 ko 5 ga watan Satumban 2018 idan hakan ya yiwa ofishin ku dai-dai.

"Mun bukacin hakan ne saboda wanda muke karewa ya riga ya shirwa hallartar wasu muhimman taruka ciki har da taron lauyoyin kasa NBA wanda ya kasance mai masaukin baki ne a taron.

"Hakan yasa zai yi masa wahala ya halarci taron kana ya amsa gayyatar duk a rana guda. Hakan yasa muke neman alfarma da a dage sauroron karar saboda wanda muke karewa ya samu damar hallarton tarukkansa."

Fani-Kayode kuma ya bukaci hukumar 'yan sandan ta bayyana masa wanda ya yi kararsa saboda hakan zai bashi daman shirya yadda zai kare kansa daga zargin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel