Babu amfanin yin mahawara tsakaninmu – APC ta maida martani ga PDP

Babu amfanin yin mahawara tsakaninmu – APC ta maida martani ga PDP

- Jam'iyyar APC ta mayar da martani ga kalubalantar ta da PDP tayi kan suyi mahawara

- APC ta bayyana hakan a matsayin abun dariya da ban mamaki

- Tace PDP bata da hurumin da zata gabatar da wannan bukata domin irin halin da ta saka kasar a shekaru 16 da tayi tana mulki

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana kalubalantar ta da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tayi na cewa suyi muhawarar kasa akan ingantaccen shugabanci a matsayin abun mamaki da ban dariya.

Idan bazaku manta ba jam’iyyar PDP ta kalubalanci jam’iyya mai mulki da Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan suyi mahawara a bainar jama’a kan ingantaccen shugabanci gabannin zabukan 2019.

Sai dai a wata sanarwa daga mukaddashin sakataren labarai na jam’iyyar APC na kasa, Yekini Nabena, jam’iyyar tace bai kamata ace jam’iyyar da ta aikata ta’asa daban-daban da baza’a iya fadi ba ta yi mahawara akan shugabanci nagari ba.

Babu amfanin yin mahawara tsakaninmu – APC ta maida martani ga PDP

Babu amfanin yin mahawara tsakaninmu – APC ta maida martani ga PDP
Source: Depositphotos

“Muna kallon wannan bukata na jam’iyyar PDP a matsayin wani abun dariya domin abunda ta saka kasar a ciki a shekaru 16 da tayi tana mulki ya isa misali,” inji APC.

KU KARANTA KUMA: An samu rabuwar kai tsakanin wasu manya a APC da Gwamnonin Jihohi

Jam’iyyar mai mulki ta kara da cewa PDP na bukatar a tunatar da ita dalilin da yasa yan Najeriya suka yi waje da ita a 2015 domin samun mulki na ci gaba, wacce a yanzu take sake gina kasar zuwa tushe mai inganci.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa daya daga cikin Dan takarar kujerar shugaban kasa na a PDP Kabiru Turaki, ya bayyana cewa jam’iyyar na bukatar daukar mutun mai martaba da mutunci a matsayin dan takarar shugaban kasa idan har tana so ta lashe zaben shugaban kasa a 2019.

Tsohon ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnatin ya fadi hakan ne a Benin, jihar Edo yayinda yake jawabi ga tawaga da mambobin PDP kan kudirinsa na takarar shugaban kasa.

Turaki yace shi ya cancanci kalubatar Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a 2019, inda ya kara da cewa kasar Najeriya na bukatar ba wai dan takara da ya san kan aiki ba kadai harda mai tarin ilimi kuma wanda baida bodadden hali.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel