Bukola Saraki ne zai iya bugawa da Shugaba Buhari ya kwana lafiya - Okupe

Bukola Saraki ne zai iya bugawa da Shugaba Buhari ya kwana lafiya - Okupe

Wani Hadimin Goodluck Jonathan a lokacin yana kan mulki ya bayyana cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ne kadai zai iya doke Shugaban kasa Muhammad Buhari a zaben 2019 domin mutanen Arewa ta tsakiya za su zabe sa idan ya tsaya.

Bukola Saraki ne zai iya bugawa da Shugaba Buhari ya kwana lafiya - Okupe

Doyin Okupe yace duk wanda Arewa ta tsakiya su ka zaba zai yi nasara a 2019

Dr. Doyin Okupe wanda yayi aiki da tsofaffin Shugaban kasar nan; Goodluck Jonathan da Olusegun Obasanjo yace zaben 2019 zai kare ne tsakanin Shugaban Majalisar Tarayya Bukola Saraki da kuma Shugaban kasa Buhari a wani bangare guda.

Okupe wanda yana cikin manyan Jam’iyyar adawa ta Accord ya bayyana cewa idan mutum na neman takarar Shugaban kasa dole ya lashe kuri’un Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas ko kuma ya lashe kuri’un Kudu da kuma tsakiyar Najeriya.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ba za ta bar Buhari yayi takara shi kadai ba

Doyin Okupe yace idan aka hada duk ‘Yan takarar Jam’iyyar adawa, za a ga cewa Bukola Saraki ne kadai ya ke da abin da ake bukata wajen tika Shugaba Buhari da kasa a 2019. Okupe yace Atiku kuma bai da jama’a sosai a Arewacin Kasar nan kamar Buhari.

Arise TV ta rahoto Okupe yana cewa Gwamna Tambuwal wanda yana cikin masu neman takarar shugabancin kasar a PDP Matashi ne amma kuma ba zai iya kai labari ba domin kuwa ba zai iya raba kan kuri’un Shugaba Buhari a Arewacin Najeriya ba.

Okupe yana ganin duk da Atiku ya shiryawa mulkin kasar nan, ba zai iya samun nasara ba don haka yake ganin babu wanda ya dace PDP ta tsaida irin Saraki. Okupe yace Saraki zai iya magana a gaban kowa a Duniya kuma ya samu karbuwa a Kudu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel