Ba sauya fasalin 'Kasa ne matsalar Najeriya ba - Osinbajo

Ba sauya fasalin 'Kasa ne matsalar Najeriya ba - Osinbajo

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito mun samu rahoton cewa, Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa matsalar da Najeriya take fuskanta a halin yanzu ba ya da wata alaka da sauya fasalin 'kasa.

A yayin da ake ci gaba da kiraye-kiraye na neman sauya fasalin kasar nan, mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa ko kadan wannan lamari ba ya daya daga cikin kalubalen da kasar ta ke fuskanta a halin yanzu.

Kazalika, mataimakin shugaban kasar ya bayyana takaicin sa gami da mamaki dangane da yadda gwamnatocin baya da suka hadar da; Ibrahim Babangida, Olusegun Obasanjo da kuma Goodluck Jonathan, suka yi bushashar su da kudaden shiga na man fetur da kasar nan ta samu a lokacin gwamnatin su.

Cikin wata sanarwa da sa hannun mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar, Mista Laolu Akande, ya bayyana cewa Ubangidansa ya fayyace hakan ne yayin ganawa da al'ummar kasar nan a birnin Minnesota na kasar Amurka a ranar Lahadin da ta gabata.

Ba sauya fasalin 'Kasa ne matsalar Najeriya ba - Osinbajo

Ba sauya fasalin 'Kasa ne matsalar Najeriya ba - Osinbajo

Osinbajo yake cewa, babbar matsalar da kasar nan ta ke fuskanta ba ta da nasaba da sauya fasali illa iyaka rashin ingatattun hanyoyi na tattali gami da ribatar alfanun albarkatun kasar nan.

A yayin da yake ci gaba da bayyana takaicin sa dangane da yadda gwamnatocin baya suka yi almubazzaranci da dukiyar kasar nan, ya kuma bayyana dalla-dalla adadin kudaden shiga na man fetur da gwamnatocin suka samu a yayin da suke karagar mulki kamar haka;

Yake cewa, "karkashin gwamnatin IBB da Abacha tsakanin 1990 zuwa 1998, an samu kimanin $199.8bn.

Gwamnatin Obasanjo da Yar'adu'a da ta gudana a tsakanin 1999 zuwa 2009, kasar nan ta samu $401.1bn.

A yayin gwamnatin Jonathan kuma tsaknain 2010 zuwa 2014, Najeriya ta samu $381.9bn."

KARANTA KUMA: Wani Mutum ya kashe kansa bayan ya sha Tabar Wiwi ta yi ma sa karo

Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa, dole gwamnati ta samar da wani yanayi wanda zai ba wa al'ummar kasar nan dama ta fahimtar iyakoki da ƙarfinta ta fuskar tattalin arziki.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a watan Yunin da ya gabata ne Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa ba bu ƙin amincewa ta bangaren gwamnatin su dangane da kiraye-kiraye na sauya fasalin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel